Rikicin Kaduna: Mutum 3 sun mutu, dayawa sun jikkata

Rikicin Kaduna: Mutum 3 sun mutu, dayawa sun jikkata

- Mutane uku sun mutu kuma dayawa sun jikkata a rikicin da ya barke tsakanin matasa a garin Kabala West Nariya da Umuazu a jihar kaduna

- Inda kiristoci sukafi yawa suna kai farmaki wa musulmai, suma musulman suna kai farmaki wa kiristoci a inda suka fi yawa

Gwamnatin Jihar ta tabbatar a jiya da cewa, an kama mutane sha takwas da ake zargi da tada tarzomar.

Wani daga wadanda abin ya auku a gabansu ya sanarwa da manema labarai cewa kafin jiyan an samu gawarwakin mutane uku a yashe a yankin da rigimar ta barke kimanin karfe biyar na asubahi,wanda hakan ne ya haifar da shirin daukar fansa da wadanda akayiwa hakan sukayi.

Ya kara da cewa, “inda kiristoci sukafi yawa suna kai farmaki wa musulmai, suma musulman suna kai farmaki wa kiristoci a inda suka fi yawa.''

NAIJ.com ta nakalto cewa Dayawa daga matafiya sun kasa giftawa ta hanyoyinsu, musamman hanyar By-Pass ta kudu da ta nufaci garin Abuja da kuma hanyar iyapot na kaduna.

KU KARANTA: Allah zai tona asirin wadanda su ka kashe Sheikh Ja’afar-Shekarau

A jawabin mai bada shawara wa gwamnan jihar gameda yada labarai, Samuel Aruwan, yace tsaro na cigaba da wanzuwa , sannan wadanda aka cafke sune kan gaba a fitinar dake aukuwa.

A cigaban bayaninsa ya nuna cewa jita-jitar cewa rikicin ya kai wasu yankunan na jihar ba gaskiya bane, ya gargadi masu yada hakan a hanyoyin sadarwa dasu kiyaye saboda illar yin hakan.

Ya nuna cewa gwamnatin jihar ta aika wakilai guraren rigimar karfafa masu tacewa a karkashin shugabancin sakataren Jihar da suka kunshi mai bada shawara na musamman gameda harkokin tsaro na cikin gida.

A rahoton NAIJ.com, wakilan sun samu ganawa da manyan yankin da ake rigimar na kungiyar Christian Association of Nigeria (CAN), Jama’atu Nasril Islam, JNI, shuwagabannin matasa, Jami'an tsaro da sarakunan gargajiyar guraren.

A karshen taron, kowanna bangare yabada amincewarsa akan duk wanda aka kama yana da hannu a tayarda zaune tsaye a tsayar masa da hukunci.

A jawabin Sarkin Aruwan Ungwan Muazu, yace rikicin ya fara ne a yayinda aka farwa wasu yan kasuwa dake dawowa gida daren lahadi,kuma a daren aka sanar dani na nemi jami'an tsaro amma basu yi komai akan hakan ba.

Kuma irin hakan shi ke haifar da rikici a Gari saboda an baiwa jama'a damar daukan doka a hannunsu.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel