Fargaba a Borno kan musayar 'yan matan Chibok

Fargaba a Borno kan musayar 'yan matan Chibok

- Mazaunar jihar Borno sun yi tsokaci kan musayar wasu kwamandojin Boko Haram da ‘yan matan Chibok

- Gwamnatin jihar ta ce samun nasarar ceto 'yan matan abin farin ciki ne da jin dadi

- Gwamnan jihar ya ce sako 'yan matan ya fitar da gwamnatinsa daga zargin da a baya aka mata na cewa sun boye 'yan matan ne

Gwamnatin jihar Borno ta yi tsokaci kan musayar 'yan matan Chibok 82 da wasu manyan mayakan Boko Haram yayin da al'umomin Arewa maso gabashin Najeriya ke bayyana fargabar sako kwamandojin.

Wasu sun yaba wa gwamnati saboda samun nasarar ceto 'yan matan da rayukansu bayan kwashe shekaru 3 a hannun mayakan na Boko Haram, inda wasu ke nuna damuwa kan hanyoyin da aka bi wajen sakin 'yan mata wanda suka ce abin tsoro ne.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Borno ta ce samun nasarar ceto 'yan matan abin farin ciki ne da jin dadi kuma hakan na tabbatar gaskiya da tsayuwar daka da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke yi a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Fargaba a Borno kan musayar 'yan matan Chibok

'Yan matan Chibok da aka kubutar daga hannun Boko Haram

KU KARANTA KUMA: Yadda sojojin Najeriya suka tsĩrar da jami'in 'yan sanda, mata 3 daga daga hannu ‘yan sata shanu

Gwamnan jihar Borno Kashim Shetima ya ce sako 'yan matan ya fitar da gwamnatin jihar daga zargin da a baya aka mata na cewa sun boye 'yan matan ne inda kuma ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan kusa sauran 'yan matan ma za su dawo ga iyayensu. Sai dai wasu al'ummar shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana damuwa kan musayar kwamandojin na Boko Haram da 'yan matan wanda suke ganin an karfafa Kungiyar ne ta yadda za su ci gaba da halaka fararen hula a yankin.

Abin tsoron shi ne ba a san su waye kwamandojin Boko Haram din da aka sake a wannan yarjejeniya ba kuma ba a san sake su abin da zai haifar wa zaman lafiya da aka samu ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali inda shugaba Buhari ke rike da jaririyar yarinya makarantar Chibok

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel