Menene ka sani game da sabon shugaban kasar Faransa Macron?

Menene ka sani game da sabon shugaban kasar Faransa Macron?

- Shugaban zai iya jan hankalin kujerar ofishinshi

- Faransa ta riga zabi mafi basira a zamninsa

- Iya maganarsa da kwaikwayo a aji ne yasa suka fara son juna shi da Brigitte

- Ba shi da gogewa a harkokkin siyasa, amma yana matsayin shugaban kasar

A wani shirin talabijin da aka yi kan sabon shugaban Faransan: wani ya ce, shugaban zai iya jan hankalin kujerar ofishinshi. Amma duk da haka sun saurare shi cikin natsuwa.

Wataran kuma yana iya gabatar da jawabi ga manyan mutane da ma matasa masu tashen gayu. Kuma su kan bashi hadin kai su saurari shi duk da basu sonshi.

Koma dai mai su ke tunani kan siyasarsa, kasar Faransa ta riga zabi mafi basira a zamaninsa. Tabbas yana da kwarjini, har'ila yau kuma ga kaifin tunani, yana kuma da kwazo da basira, matashi ne mai kyakyawan fata wanda bai yadda da cin hanci ba.

KU KARANTA: Chelsea na daf da zama zakarun Ingila

A duk lokacin da ka saurari jawabin Macron sai kaji ka gamsu da maganarsa. Mutane kan yi mamakin abubuwan da yake fada. Bututwan da yake magana a kansu duk haka suke. Amma me yasa ba mu yi tunanin haka a baya ba.

Ya auri Brigitte Trogneu, malamarsa ,wacce ta girmesa da shekara 24.

Emmanuel Macron kamar Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, bai yarda da cin hanci da rashawa ba

Emmanuel Macron kamar Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, bai yarda da cin hanci da rashawa ba

Yanzu yana da shekara 39, duk da cewa ba shi da gogewa a harkokkin siyasa, amma yana matsayin shugaban kasar da ita ce ta biyar a kasashen a duniya.

Shin akwai wanda zai ga laifinshi idan ya naji kamar a kwai wanda ke idon kansa?

Zaben sabon shugaban kasar ba shi ne lokacin da ya jawo mutane suka nuna suna sonshi ba, kuma yawancin mutane za suyi fatan alkhairi ga mutumin da yake nagari mai kyakkyawar dabi'a, domin suna bukatar wanda zai sadaukar da kanshi ga kasar.

KU KARANTA: Tofa: Wani Ministan Buhari ya shiga uku

Sai dai idan akwai wata ayar tambaya akan Emmanuel Macron, to ba zai wuce wasu abubuwa na musamman da suke tattare da shi ba.

Baiwarsa ta iya magana (Ka tuna cewa iya maganarsa da kwaikwayo a aji ne yasa suka fara son juna shi da Brigitte).

NAIJ. Com ya samu labari cewa, sau da yawa abin da yake sawa jama'a fargaba da Macron shi ne kalmomin da yake amfani da su, sune su ke yi masa aikinsa.

Furuci ne da suke dinke baraka, da furucin kuma suke tausasa abokan adawarsa.

A lokacin yakin neman zabe, sau da yawa yana hada amsoshinsa da kalmomin "a lokaci guda" inda hakan ya zama abin zolaye a tsakanin 'yan jarida.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan NAIJ.com bidiyo na nuna shafin sanarwan Buhari na zaben 2019 shin ta yi saurin fitowa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel