Kungiyar Chelsea na shirin daukar kofin firimiya

Kungiyar Chelsea na shirin daukar kofin firimiya

– Kungiyar Chelsea na daf da daga kofin firimiya na Ingila

– Yanzu nasarar wasa guda kurum Chelsea ke bukata

– Hakan ya zo bayan Chelsea ta lallasa Kungiyar Middleborough

Yanzu dai Chelsea ta kama hanyar lashe gasar Firimiya.

Kungiyar Chelsea na neman maki uku ne rak domin zama zakara.

Dan wasa Nemanja Matic yace har yanzu ba za su ce sun ci gasa ba.

Kungiyar Chelsea na shirin daukar kofin firimiya

Kungiyar Chelsea sun taja rawar gani

Chelsea za ta iya lashe gasar Firimiya na shekarar bana daga ta samu maki uku kacal cikin wasannin da su ka rage. Tottenham Hotspur ne dai ke bin Kungiyar sau-da-kafa a baya sai da alamu ba za ta kamu ba.

KU KARANTA: Dalar Amurka ta tashi sama

Kungiyar Chelsea na shirin daukar kofin firimiya

Diego Costa na Kungiyar Chelsea

Hakan ya zo ne bayan Chelsea ta ba Kungiyar Boro kashi a wasan da su ka buga jiya da dare. Chelsea ta doke Boron ne da ci uku da nema wanda duk Fabregas ne ya haddasa su. KungiyarChelsea za ta kara da Wes Brom Ranar Juma’a.

Su ma zakarun UEFA Champions league Kungiyar Real Madrid na iya kafa tarihi idan su ka kara daga kofin a bana. Babu wanda ya taba daukar kofin dai sau biyu a jere tun da aka sauya Gasar na zakarun Turai.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dabarar kashe kudi da adana?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad
NAIJ.com
Mailfire view pixel