Ga abin takaici da ya biyo bayar doka na hana yawo da dabbõbin a jihar Binuwai

Ga abin takaici da ya biyo bayar doka na hana yawo da dabbõbin a jihar Binuwai

- Ta ce mutane 3 ne aka kashe yayin da wasu da dama suka jikkata

- An tattara cewa makiyayan suka fara harbe-harbe a kauyen

- Maharan ne aka ce sun zo daga yankin Taraba, ta hanyar Abaji

- Zan iya tabbatar muku da cewa an mayar da zaman lafiya a can yanzu

Mutane 3 ne aka tabbatar makiyayan a kauye Tse-Akaa, yankin Ugondo Mbamar na karamar hukumar LogoJihar Binuwai sun kashe.

Wannan yana zuwa a 'yan kwanaki bayan da majalisar dokokin jihar Benue ta kafa doka na hana yawo da dabbõbi da kuma kiwon dabbobi a waje a jihar.

NAIJ.com ya tara cewa matsala ta fara kewaye da 2:00 a ranar Lahadi, yayin da makiyayan, wanda suna yawo da shanunsu daga yankin suka yi karo da wasu mutanen wani kauye. An tattara cewa makiyayan suka fara harbe-harbe a kauyen.

KU KARANTA: An gurfanar da matan da ta rotsawa tsohon saurayinta kai da karfe

Margaret Acka, wata majiya daga yankin, ta ce mutane 3 ne aka kashe yayin da wasu da dama suka jikkata da makiyayan,, a rikicin da ya bari yawan mutane suka dinga shan mafaka a kauye dake kusa.

Kashe-kashen na zuwa a 'yan kwanaki bayan da majalisar dokokin jihar Benue ta kafa doka na hana yawo da dabbõbi da kuma kiwon dabbobi a waje a jihar

Kashe-kashen na zuwa a 'yan kwanaki bayan da majalisar dokokin jihar Benue ta kafa doka na hana yawo da dabbõbi da kuma kiwon dabbobi a waje a jihar

A cewar Acka, "Fulani makiyayan sun zo gidan mahaifina a yau (Lahadi) da rana suna harbi suka kuma kashe mutane 3 da wasu da dama sun samu rauni. Yaushe wannan zai zo karshe? "

Wani mashaidi, James, ya ce da makiyayan suka kaddamar da hari game da karfe 5na yanma jiya kawai da ‘yan kauyen na fitowa daga Coci ran Lahadi da yamma bayan sabis.

KU KARANTA: Jami'in kwastom ya rataye kansa a daki a garin Gwarimpa Abuja

Maharan ne aka ce sun zo daga yankin Taraba, ta hanyar Abaji, Mbamar, Ugondo da suka fita a Akaa, suna harbi zuwa kasuwar kauyen.

Lokacin da aka tuntubi, rundunar 'yan sandan jihar , (PPRO), ASP Musa Yamu wanda ya tabbatar da rahoton, ya ce, makiyaya Fulani da ake zargin sun ƙaura daga yankin a sakamakon farko zuwa kakar ruwa yana daga nan suka yi karo da 'yan kyauyen.

Ya ce: "Mutane 3 ne aka kashe a cikin rikicin amma 'yan sanda nan da nan sun hada zuwa yankin da kuma zan iya tabbatar muku da cewa an mayar da zaman lafiya a can yanzu."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan NAIJ.com bidiyo na nuna yadda rikicin Ile-Ife ya faru

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel