Ra’yoyin ‘yan Najeriaya game da tafiyar Buhari zuwa Landon

Ra’yoyin ‘yan Najeriaya game da tafiyar Buhari zuwa Landon

- ‘Yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da tafiyar shugaba Buhari zewa Landan

- A cewar wasu ‘yan Najeriya ya kamata Buhari ya yi murabus saboda yanayin rashin lafiyarsa

- Wasu kuma sun ce zasu ci gaba da yiwa shugaban addu’a

Shugaba Buhari ya tashi Najeriya a daren ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu don ya ci gaba da kiwon lafiyarsa a kasar Birtaniya.

Wannan ne karo na uku da shugaban zai yi tafiyar hutun ganin likita tafiya da shugaba tun da aka ransar da shi a matsayin shugaban kasa a watan Mayu 2015.

A baya shugaban ya yi irin wannan tafiyar domin ganin likita a Landon ya shafe kwanaki 51 wannan tafiyar ta haifad da muhawara tsakanin 'yan Najeriya..

Ra’yoyin ‘yan Najeriaya game da tafiyar Buhari zuwa Landon

Shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo kafin tafiyarsa zuwa Landon

A wannan tafiyar shugaban kasar zuwa Landon ma an fara wani cece-kuce da kuma muhawara tsakanin 'yan Najeriya yayin da wasu ke kiran shugaban da yin murabus saboda yanayin rashin lafiyarsa.

Amma wasu magoya bayan shugaba Buhari na cewa suna bayansa kuma suna tayashi da addu’a, cewa rashin lafiyarsa ba komai bane ila tsufa.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo, Bukola da Dogara sunyi bankwana wa shugaba Buhari a tafiyarsa

NAIJ.com ta tattaro wasu da cikin ra’yoyin ‘yan Najeriya:

Kelvin ya rubuta a shafin zumunta na twitter cewa: “Allah ya kara sauki shugaba kasar; shugabanci nada wahala”.

Babadee shi kuma ya ce: "Idan kasan ba kada lafiya, ka sauka daga kan mulki".

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Landon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel