An hana manema labarai shiga dakin taron da Buhari ya gana da 'yan matan Chibok

An hana manema labarai shiga dakin taron da Buhari ya gana da 'yan matan Chibok

- Jami’an tsaron fadar gwamnatin tarayya sun hana manema labarai shiga liyafar karba ‘yan matan Chibok a Aso Rock Villa

- Mai daukar shugaban kasa hoto na musamman wanda kuma wakilin gidan talabijin NTA kawai ya samu shiga dakin taron

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi ba unci ‘yan matan makaranta Chibok 82 da Boko Haram ta sake a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu a fadar gwamnati.

Jami’an tsaro sun hana manema labarai fadar gwamnati shiga dakin taron da shugaban kasa ke kanawa da ‘yan matan Chibok.

NAIJ.com ta ruwaito cewa wakilin gidan talabijin na kasa NTA, wanda shine kuma musamman mai daukar shugaban kasa hoto, Bayo Omoboriowo kawai aka ba damar shigar dakin taron. Sai kuma akwai wasu ‘yan jaridar kasashen waje da aka ba izinin shiga.

An hana manema labarai shiga dakin taron da Buhari ya gana da 'yan matan Chibok

Shugaba Buhari da 'yan matan Chibok a fadar gwamnatin tarayya

Kasancewa a dakin taron ne shugabannin jami’an tsaro da kuma wasu jami'an gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Shugabar matan APC ta jinjinawa Shugaba Buhari a yanto yan matan Chibok da akayi

Wannan shi ne karo na farko da za a hana yan jarida a fadar gwamnati shiga liyafar kan 'yan matan Chibok da aka sake.

Yan jarida wanda sun kasance a kofar shigar Villa ta aso rock tun fiye da sa’o’i 4 aka hana su daga ganin fuskokin 'yan matan wanda ministan harkokin mata Aisha Alhassan ta jagorancin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga-zangar kan rikice-rikicen banbancin jinsi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel