Ba gazawa bane fitar Shugaba Buhari domin lura da lafiyarsa - Imam

Ba gazawa bane fitar Shugaba Buhari domin lura da lafiyarsa - Imam

- Babban limamin Masallacin Juma'ar Nupe Road ya kalubalanci masu surutai gameda kulawar da shugaban kasa keyiwa lafiyarsa da cewa su kiyayi aukawa fushin Allah

- A maimakon bata lokacin yada abinda zai janyo zunubi , addu'o'i ya kamata mu rika taimakawa dasu wa lafiyar shugaban

Mazaunin garin kaduna, Malam Muhammad Nafi’u ya kalubalanci masu surutai gameda kulawar da shugaban kasa keyiwa lafiyarsa da cewa su kiyayi aukawa fushin Allah.

Malam Nafi’u, Babban limamin Masallacin Juma'ar Nupe Road, dake kaduna yayi furucin ne a a tattaunawar da akayi dashi gameda tsokaci akan lafiyar shugaban.

NAIJ.com ta nakalto yace: “In Buhari bashi da lafiya, neman waraka ba laifi bane a gareshi, shi mutum ne kamar kowa daga cikin mu.

“Laifi ne yada jita-jita da maganganun da basu tabbata ba a shari'ance, rashin lafiya bata bar kan kowa ba, a sakamakon haka mutane su kiyaye bakunansu daga irin hakan.

“A maimakon bata lokacin yada abinda zai janyo zunubi , addu'o'i ya kamata mu rika taimakawa dasu wa lafiyar shugaban.''

KU KARANTA: Obanikoro ya hadu da Tinubu domin shiga jam'iyyar APC

Ya kara da cewa: ''Shugaban ya nuna matukar lura da kauna wa mutan kasa baki daya saboda haka muma babbar hanyar saka masa itace addu'a.

“Shugaban mu na bukatar kasantuwa cikin koshin lafiya domin domin da lafiayar ne kyautatuwar mulkin na kasa baki daya zai gudanu. Allah ya bamu shugaba kam sai dai muyi adu'ar Allah ya tabbatar mana dashi.''

Imam din ya nemi yan najeriya da suyi kokari gurin cigabantarda hadin kai da kyautatawa juna zato tareda fatan Alhairi wa shugaba buhari.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko ta twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel