DSS ta saki tsohon kwamnan jihar Binuwe

DSS ta saki tsohon kwamnan jihar Binuwe

- Jami’an tsaro ta DSS ta ce ta saki tsohon gwamnan jihar Binuwe wanda yake tsare tun watan Fabrairu

- An kama Suswan ne kan wasu abubuwa da aka gano a cikin motoci a wani gida a Abuja, wanda ake zato malakar shine

- Ana zargin Suswam da kwamishinan kudi, Omodachi Okolobia da yin awon gaba da biliyan 3.1 na jihar

Jami’an tsaro ta farar hula, DSS ta saki tsohon gwamnan jihar Binuwe, Gabriel Suswam dangane da kai-fitarwa.

Kafin a saki tsohon gwamnan a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu, Suswam ya kasance a tsare na kwanaki 71 yayin da ‘yan sanda siri ta kama shi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, an kama tsohon gwamnan ne kan wasu abubuwa da aka gano a cikin motoci a wani gida a Abuja, wanda ake zato malakar shine.

DSS ta saki tsohon kwamnan jihar Binuwe

Tsohon gwamnan jihar Binuwe, Gabriel Suswam

KU KARANTA KUMA: Ofisha hukumar kwastam yayi kisan kai a garin Gwarinpa, Abuja

Rahotanni daga DSS ta nuna cewa jami’an ta samu motoci 45, takaddun shaida na mazauni 21 da kuma makamai da harsasai a lokacin binciken wani gida mai adireshi 44, Aguiyi Ironsi Way, Maitama, Abuja.

Ana zargin Suswam da sace wasu kudin jihar Binuwai biliyan 3.1 na hannun jari a manyan kamfanoni tare da kwamishinan kudi, Omodachi Okolobia.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel