Abubuwa 3 da ake tsammani Osinbajo ya fara da su

Abubuwa 3 da ake tsammani Osinbajo ya fara da su

– Farfesa Osinbajo ya zama mukaddashin shugaban kasa

– Ana tsammani ya fara wasu ayyuka da ya zaran ya shiga Ofis

– Akwai maganar Sakataren Gwamnati dsr

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma asibiti

Fadar shugaban kasar tace babu abin tada hankali domin Osinbajo zai ja ragama

Daga cikin abubuwan da zai fara tabawa watakila akwai:

Abubuwa 3 da ake tsammani Osinbajo ya fara da su

Buhari ya koma Landan domin ganin Likita

1. Sakataren Gwamnati

Farfesa Osinbajo ya jagoranci kwamitin da aka nada domin binciken Babachir Lawal kuma an sa rai a mikawa shugaban kasar rahoto a yau. Watakila mukaddashin shugaban kasar ya dauki mataki game da kujerar da kuma Babachir da aka dakatar.

KU KARANTA: Osinbajo ya larbi ragamar mulkin kasa

2. Kasafin kudi

Har an shiga watan Mayu amma Majalisa ba ta amince da kasafin kudin shekarar bana ba. Yayin da lokacin ke kurewa ba mamaki mukaddashin shugaban kasar ya gana da shugabannin Majalisa.

Abubuwa 3 da ake tsammani Osinbajo ya fara da su

Osinbajo tare da Buhari jiya a Villa

3. Sababbin Ministoci

Majalisar Dattawa ta tantace Farfesa Ikani Ocheni da Sulaiman Hassan a matsayin Ministocin Najeriya domin maye gurbin Amina J. Mohammed da Marigayi James Ocholi. Ana sa rai Osinbajo ya zabi ma’aikata ya bayyana ofishin da za su fara aiki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wa za a zaba a zabe mai zuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel