Ofisha hukumar kwastam yayi kisan kai a garin Gwarinpa, Abuja

Ofisha hukumar kwastam yayi kisan kai a garin Gwarinpa, Abuja

- A kauyen Lungu, Gwarinpa dake Abuja ne Assistant Superintendent (ASC) na kwastom ya kashe kansa

- CSP Nuruddeen Sabo na Hukumar yan sandar yankin Gwarinpa ya shedawa manema labarai cewa an tabbatarda mutuwar mutumin ne a Kubwa General Hospital

Har yanzu dai ba'a gama tantance dalilin da yasa yayi kisan kan nasa ba a cewar rahoto.

Majiyar labarai ta nuna cewa mutumin dan shekara 44 ya kulle kansa ne a a daki tareda rataye kai da igiya a ranar asabar da ta wuce.

A wata majiyar ta NAIJ.com ta nuna cewa shi mamacin, da bai taba aureba na zama ne tareda da'uwansa kafin yi masa taransafa zuwa jihar legas ba da dadewa ba kafin aukuwar abin.

KU KARANTA: Abin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gaya 'yan matan Chibok 82 a bayan kofofi kafin tafiyarsa zuwa Ingila

CSP Nuruddeen Sabo na Hukumar yan sandar yankin Gwarinpa ya shedawa manema labarai cewa da'uwan nasa na shagon wani mai aski a yayinda aika-aikan ya auku. an tabbatarda mutuwar mutumin ne a Kubwa General Hospital.

“Daga dangin kayan zargi da aka samu tareda shi akwai kwayoyi da wukake , masu bincike dai sun nuna cewa daga dalilan kisan kan akwai kasancewar mamacin a cikin damuwa da kunci.''

Ku biyomu ta Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel