Mai aiki ta sanya guba cikin abincin maigidanta

Mai aiki ta sanya guba cikin abincin maigidanta

Wata mai aiki yar shekara 14 tayi kokarin hallaka maigidanta, Nasiru Akinlosotu, ta hanyar garwaya maganin bera da abincinshi saboda yayi mata fada.

Hukumar yan sanda ta damke yarinyar wacce dalibar firamarece a makarantan gwamnati a jihar Ondo.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa mutumin wand mazaunin titin Adetomowo a jijar ya tsallaka rijiya da baya ne da ikon Allah.

Uwargidansa, SIkirat, ta umurci yar aikin ya girgawa mijinta abinci kain ta dawo daga shago.

Yarinyar bayan ta gama girkin, sai ta sanya guba cikin abincin mijin. Shi kuma sai ya farga ta hanyar warin da abincin keyi. Da aka tuhume ta, sai ta tona asirin kanta a gaban makwabta.

Mai aiki ta sanya guba cikin abincin maigidanta

Mai aiki ta sanya guba cikin abincin maigidanta

Mutumin yace:

“Na rigaya da cin cokali daya a baki na. ina gab da hadiyewa sai na ji wani wari mara kyau daga cikin abincin.

“Da wuri sai na amayo abincin kuma na kirata domin tambayanta abinda ya faru. Sai tace mini ai saboda wasu sinadari da ta sa ne.”

KU KARANTA: AN yankewa wasu barayin shanu hukuncin kisa

Yace wanna amsa nata bai gamsar da shi ba, sai ya gayyaci makwabta.

“Da makwabta sukayi mata tambayoyi, sai ta bayyana cewa lallai ta sanya maganin beran da uwargidata ta saya a cikin abincina saboda ramuwa da fadan da na mata kwanakin baya.

“Bayan hakan, sai na fadawa matana. Sai ta kai kara ofishin yan sandan unguwar Yaba."

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Femi Joseph, yace an kawo karan zancen ofishin ta jihar.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel