Yan matan Chibok: Jonathan ya jinjinawa aikin shugaba Buhari

Yan matan Chibok: Jonathan ya jinjinawa aikin shugaba Buhari

- Jonathan yace wannan ya nuna kokarin Buhari da yunkurin yantar da dukanin yan kasa,ba ma yan cibok kadai ba daga wani mummunan hali da suke iya shiga

- Sakin yara matan zai taimaka kwarai gurin kwantarda tashin hankali da halin damuwa da iyayensu ke ciki tsawon shekaru uku

Mr Taidi Jonathan, tsohon ciyaman na kungiyar lauyoyin kasa na garin Minna yace sakin yan matan Chibok 82 ya nuna cika alkawarin da shugaba Buhari yayiwa najeriya na lura da hakkokinsu.

NAIJ.com tace Taidi a tattaunawar da akayi dashi yace wannan nuni ne ga cewa shugaban na iya yanto da dukkanin wadanda ake tunanin sun shiga tsaka mai wuya ko hannun yan ta'adda.

“Wannan ya nuna kokari da yunkurin yantar da dukanin yan kasa,ba ma yan cibok kadai ba daga wani mummunan hali da suke iya shiga.

“Sakin yara matan zai taimaka kwarai gurin kwantarda tashin hankali da halin damuwa da iyayensu ke ciki tsawon shekaru uku.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bar wasiyya kafin ya shilla zuwa Ingila

Jonathan, ya kira yan najeriya mabanbanta adiinai da siyasa dasu bawa gwamnati mai ci kwarin guiwa a kokarin tabbatarda zama lafiya da magance tashin-tashina a kasa.

tsohon shuganan na ya nemi yan Najeriya da su cigaba da addu'a gameda halin da kasar ke ciki tareda kyautata zaton samun nasara bada dadewa ba.

Jonathan ya kara da cewa yan kasa su saba da kokarin taimakawa jami'an tsaro da bada bayanin dukkanin masu kokarin tada zaune tsaye a dukkanin bangarorin kasar.

NAIJ.com tace rahotanni sun Nuna shekarar 2014 cewa Boko Haram sun kame yan mata sama da 200 a Government Girls’ Secondary School, Chibok, Borno.

An saki ashirin daga cikinsu ne a watan Oktoba 2016, a yayinda Buhari bada umarnin cewa a tabbatarda sauran ma an samesu don sadarda su ga ya'uwansu.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko ta twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel