Obanikoro ya hadu da Tinubu domin shiga jam'iyyar APC

Obanikoro ya hadu da Tinubu domin shiga jam'iyyar APC

- Sanata Musiliu Obanikoro, tsohon ministan tsaro na cikin gida, ya yanke shawarar barin tsohuwar jam'iyyarsa da ya shiga shekaru goma da suka wuce

- A yan kwanaki kadan sanata Obanikoro zai zama cikakken dan jam'iyyar ta APC a Jihar Legas

Obanikoro, dan takarar gwamna a shekarar 2011 karkashin jam'iyyar PDP a legas ya na dap da komawa karkashin inuwar All Progressives Congress (APC).

a wata majiyar an tabbatarda cewa koro, kamar yarda a ke takaita sunansa zai zama cikakken dan jam'iyyar ta APC a kwanaki kadan nan gaba.

a wata majiyar NAIJ.com daga PDP ta jihar legas,sunce APC na nan na kulle-kullen makircin cigaba da shigo-shigo da sukewa Obanikoro a jam'iyyarsu a wannan satin. daga dalilan da suka sa za'a iya yarda da shigarsa jam'iyyar akwai tasirantuwar bibitar da yayiwa jigon jam'iyyar ta APc wato Bola Ahmed Tinubu.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Adam A. Zango yayi wa addinin musulunci gagarumar hidima

A farkon lamarin Tinubu ya kyamaci hakan , amma daga bisani bayan ya tuntubi wasu daga manyan Jam'iyyar an samu shawowa kan Tinubun.

Bayan Haduwarsun ne tareda shiga tsakanin da shuwagabannin addinai da sarakunan legas yasa Obanikoro yasami karfin guiwar fara shirye-shiryen zama cikakken dan jam'iyyar.

Obannikoro ya bada hakuri da uzururruka gameda adawa,rashin kunya da shaguben da yayi musu a lokacin baya, kuma a karshe Tinubun ya nuna ya yafe masa kurakurensa.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel