Yan bindiga sun yi garkuwa da uwar wani ɗan majalisa

Yan bindiga sun yi garkuwa da uwar wani ɗan majalisa

-Yan bindiga sun yi awon gaba da mahaifiyar wani dan majalisar jihar Nassarawa

-Yan bindigan sun bukaci a biyansu naira miliyan 30

Wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun sace mahaifiyar dan majalisa dake wakiltar mazabar Akwanga ta kudu a majalisar jihar Nassarawa Kassim Mohammed-Kassim, a daren Asabar 6 ga watan Mayu, inji rahoton Premium Times.

Kaakakin rundunar yansandan jihar Nassarawa Kennedy idrisu ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labaru, NAN a ranar Lahadi a garin Lafia.

KU KARANTA: ‘Dalilai 6 dake nuna bai kamata a saki ýan Boko Haram saboda ýan matan Chibok ba’ – PDP

NAIJ.com ta ruwaito Kaakakin yana fadin cewar yan bindigan sun dira gidna dan majalisar ne a garin Akwangan da misalin karfe 8 na dare, inda suka yi harbi a sama daga nan suka wuce da matan su biyu.

Yan bindiga sun yi garkuwa da uwar wani ɗan majalisa

Yan bindiga

“A yanzu haka yansanda suna sintiri a yankin a kokarinsu na kubutar da matan tare da kama masu laifin” inji shi.

Sai dai Kaakakin ya bukaci al’umma dasu taimaka musu da bayanai da suka danganci matan, domin saukaka musu aikinsu.

A wani hannun kuma, wata majiya daga dangin dan majalisar ta shaida cewar yan bindigan sun kira waya, sun bukaci a biya su naira miliyan 30, amma dai dan majalisar bai tabbatar da hakan ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Manoma sun koka kan hare haren da ake kai musu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel