Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

Kamar a jiya ko shekaranjiya ne aka rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya kayar da shugaban kasa na wancan lokaci, Goodluck Ebele Jonathan.

Amma za a iya cewa kusan shekara biyu kenan, tun bayan nasarar da jam’iyyar adawa ta APC ta samu a kan jam’iyya mai mulki PDP a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a cikin watan Maris, 2015.

NAIJ.com ta samu daga majiyar ta ta Premium Times Hausa cewa ba a zaben shugaban kasa kadai PDP ta sha mummunan kaye ba, har ma da zaben gwamnoni, inda a Arewa ta tsira da jihohi biyu tal, da yarfe gumin goshi, wato jihohin Gombe da Taraba.

Tashin farko dai ya kamata mai karatu ya san cewa dukkan ‘yan takarar PDP da na APC duk daga Arewa za su fito.

1. MUHAMMADU BUHARI:

Buhari zai iya maye gurbin Buhari idan aka yi la’akari da abubuwa da dama. Na farko dai har yau bai fito ya ce ba zai iya sake tsayawa takara ba. Na biyu kuma ‘ya’yan jam’iyyar APC manya da kanana za su so a ce shi ne ya kara tsayawa, domin da dama saboda albarkacin sa ne aka ci zabe, dalilin furucin sa na cewa a yi “sak” a lokacin zaben 2015.

Don haka idan ba Buhari ba ne, zai yi wahala talakawan da suka saida ran su saboda Buhari, su sake irin dukan jikin su da danyen kara kamar yadda suka yi a 2015.

Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

2. ATIKU ABUBAKAR:

Ko shakka babu, Atiku Abubakar ya na son zama shugaban kasa, idan aka yi la’akari da cewa ya taba yin takara har sau uku baya. Ya yi a 2007 karkashin jam’iyyar ACN, a 2011 ya fadi a zaben fidda-gwani na PDP, a 2015 kuma ya fadi a zaben-fidda-gwanin APC.

Babu ko tantama Atiku mutum ne mai karfin siyasa da kuma karfin arziki. Cikakken dan kasuwa ne wanda karfin Dangote ne ya dusashe karfin arzikin sa a Nijeriya, shi ya sa ba a saka shi cikin manyan attajirai. Watakila saboda kallon da ake masa na dan siyasa.

3. RABIU MUSA KWANKWASO:

Idan ana maganar gwarzon iya kokawar siyasa, tilas a saka tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a sahun gaba. Ya kasance shi da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi ne suka fi shigewa hancin Shugaba Goodluck Jonathan, kuma ya kasa fyace su, har sai da suka hada masa jibi da majina.

Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

Kwankwaso tsohon dan siyasa ne, ya taba rike mataimakin shugaban majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar SDP. Shi ne ya yi gwamnan Kano a 1999 zuwa 2003 a karkashin jam’iyyar PDP. Sai dai ya na kan mulki abokin takarar san a jam’iyyar ANPP, Malam Ibrahim Shekarau ya kayar da shi a zaben 2003.

4. NASIRU EL-RUFA’I:

Gwamnan Jihar Kaduna na yanzu Nasir El-Rufai ya na da damar maye gurbin Buhari idan har aka tsaida shi takara. El-Rufai wukar yanka giwa ce, wadda ba girma ake bukata ba, sai kaifin ta. Shi ne mutum na farko da ya fara aikin gyara na ba-sani-ba sabo a Abuja lokacin ya na Minista na Babban Birnin Tarayya. Mutum ne kuma mai kokarin bin tsarin doka ba dan-ta-ci-barkatai ba ne.

5. NUHU RIBADU:

Idan ta yi wani juyin har aka ba Nuhu Ribadu takara, to zai iya maye gurbin Buhari. A matsayin sa na Shugaban EFCC, ya kasance bai tsohon kama kowa a kasar nan. Har Ogan sa Tafa Balogun sai da ya sa wa ankwa. Mutum ne wanda bai yarda da cin hanci ba, kuma ya sha nanatawa cewa tun da ya ke bai taba karbar cin hanci ba, idan akwai mai shaida to ya fito ya karyata shi. Ribadu na da goyon baya har a Kudancin kasar nan.

Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

Duk da cewa a yanzu dai ba boyayye bane a fagen siaysar Najeriya domin yana daya daga cikin wadanda suka fafata a 2011 lokacin da ya fito takaran shugabancin kasa Najeriya a jam’iyyar ACN.

6. BUKOLA SARAKI:

ar tayi karfin da ko shugaban kasa a wancan lokacin sai ya nemi shawarar gwamnoni kafin ya aiwatar da wasu ayyuka.

Bukola yana daya daga cikin wadanda sukayi ruwa sukayi tsaki don ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a 2015.

Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

Yan arewa 7 dake hankoron maye gurbin shugaba Buhari a 2019

Shine shugaban Majalisar dattijai kuma iya siyasar sa ta sa ya samu karfin da yadda yake so a majalisar haka akeyi.

Babban Matsalar da Bukola zai iya samu a zaben da ke tafe idan har zai yi takarar shugaban kasa shine laifukkan cin hanci da rashwa da handame kudaden gwamnati da ake zarginsa da yi wanda har yanzu yana fuskantar shari’a a kotun kula da da’ar ma’aikata, CCT.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sanata Shehu Sani ya lissafa wasu muhimman matakai daya zama wajibi a ɗauka don sake raya Arewa

Sanata Shehu Sani ya lissafa wasu muhimman matakai daya zama wajibi a ɗauka don sake raya Arewa

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel