Shugaba Buhari ya bar wasiyya kafin ya shilla zuwa Ingila

Shugaba Buhari ya bar wasiyya kafin ya shilla zuwa Ingila

- A yammacin jiya, Shugaba Buhari ya karbi bakunci mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da kuma kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara

- Ya karbi bakuncin nasu ne kafin tafiya ya shilla Landan a daren jiya.

Inda Shugaba Buhari ya shaida musu cewa “Ina da cikakken yaƙinin za a tafiyar da Gwamnati cikin tsari yadda ya kamata yayin da ba na nan. Allah Ya albakaci Nijeriya.

NAIJ.com ta tuna cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake komawa Ingila domin likitoci su duba lafiyarsa.

Sanarwar da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar, ta ce shugaban zai gana da likitocin ne a wani bangare na ci gaba da jinyar daya je a watannin baya.

Shugaba Buhari ya bar wasiyya kafin ya shilla zuwa Ingila

Shugaba Buhari ya bar wasiyya kafin ya shilla zuwa Ingila

KU KARANTA: Dalilai 7 da yasa aka saki yan matan Chibok

Sai dai ya ce babu tabbacin ranar da shugaban zai dawo domin likitoci ne kawai za su fayyace hakan.

Amma ya ce ka da 'yan kasar "su tayar da hankulansu domin babu wani abin damuwa".

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ne zai ci gaba da mulkin kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

Kuma tuni shugaban ya "aika wasika ga majaisar dattawa" domin sanar da su cewa Osinbajo ne zai ci gaba da lura da al'amura.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau
NAIJ.com
Mailfire view pixel