Wasu hatsabiban yan bindiga sun mamaye sansanin yan sanda

Wasu hatsabiban yan bindiga sun mamaye sansanin yan sanda

- Wasu yan bindiga da suka dade suna kai hare-hare a yankunan dake gabar ruwa a jihar Ogun, sun kai hari a sansanin yan sandan ruwa dake jihar, inda suka kashe dan sanda daya.

- Mutumin da aka kashe mai suna Sajan Segun Akinola

Yan bindigar dauke da manyan makamai sun isa sansanin a daren ranar Alhamis, inda suka harbe yan sanda biyu tare da yin gaba da jirgin ruwa mai dauke da bindiga na rundunar yan sandan.

NAIJ.com ta samu labarin wani dan sanda daya tsira da ransa yace baza su iya maida martani ba, saboda basu da isassun makamai.

“yan bindigar sun zo sansanin da shirin su dauke da manyan makamai,inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi,wanda ya rutsa da Sajan Akinola”yace.

Wasu hatsabiban yan bindiga sun mamaye sansanin yan sanda

Wasu hatsabiban yan bindiga sun mamaye sansanin yan sanda

“An harbe wasu yansandan guda biyu inda aka garzaya da su zuwa asibiti”

Harin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan yan bindigar sunkai hari gidan wani attajiri da ke yankin,tare da kashe yan kungiyar tsaro ta Sakai 3 a yayin kai harin.

Shugaban karamar hukumar Ogun water Side Femi Onanuga ya bayyana damuwarsa kan yawan hare-hare da ake kaiwa a yankin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel