‘Dalilai 6 dake nuna bai kamata a saki ýan Boko Haram saboda ýan matan Chibok ba’ – PDP

‘Dalilai 6 dake nuna bai kamata a saki ýan Boko Haram saboda ýan matan Chibok ba’ – PDP

-Jam'iyyar PDP ta nuna rashin amincewarta da yadda gwamnati ta musanya yan Boko Haram da yan matan Chibok

-PDP ta ce an karya dokokin kasa da kasa daya haramta shiga yarjejeniya da yan ta'adda

Tsagin sanata Ahmad Makarfi na jam’iyyar PDP ta taya iyaye da yan uwan yan matan Chibok murnan kubutar da yan matan da gwamnati tayi daga hannun kungiyar Boko Haram.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne ta bakin kaakkinta Dayo Adeyeye wanda ya shaida cewar jam’iyyar na farin cikin sake saduwar yan matan da iyayensa bayan kwashe shekaru 3 a hannu, sai dai PDP ta nuna bacin ranta da yadda aka yi canjin yan matan da wasu yan Boko Haram.

KU KARANTA: Buhari ya sa labule da Osinbajo, Saraki da Dogara a fadar gwamnati kafin ya wuce ƙasar Ingila

Da haka ne jam’iyyar ta soki gwamnati domin yin musayar yan Boko Haram da matan Chibok da tayi, kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto, kuma jam’yyar ta zayyana dalilanta guda 6 kamar haka:

1). Hakan na nufin yan ta’addan sun sha kenan, kuma ba za’a hukun tasu ba, don haka duk kokarin da hukumomin tsaro ya tashi a banza kenan.

‘Dalilai 6 dake nuna bai kamata a saki ýan Boko Haram saboda ýan matan Chibok ba’ – PDP

Sanata Makarfi

2). Sakin yan matan Chibok din ya alamta cewar zasu koma bakin daga kenan a cigaba da fafatawa dasu, ko kuma su cigaba da taimaka ma Boko Haram wajen daukar yan ta’adda da tada bamabamai.

3). Hakan ya kara ma Boko Haram kwarin gwiwa kenan, kuma zasu cigaba da amfani da dabarar yin garkuwa da yan Najeriya, don su dinga musayar su da mutanen su da aka kwace.

4). Yadda Boko Haram ke sakin yan matan kadan kadan na nufin zasu cigaba da neman bukata daga gwamnati kenan.

5). Sako yan matan zai kara ma iyayen wadanda basu fito ba damuwa, don haka sai yafi dacewa ace an sako yan matan gaba daya.

6). Musayar yan ta’ddan Boko Haram da yan matan Chibok ya saba da dokokin kasashen duniya dake cewa kada a sake a shiga wata yarjejeniya da yan ta’adda.

Daga karshe jam’iyyar PDP tace duk da cewa ta gamsu da manufar Buhari na kubutar da yan matan Chibok, amma ya bata rawarsa da tsalle musamman yadda yayi musayar yan matan Chibok da yan ta’addan Boko Haram.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Saurari ra'ayin wani dan Najeriya game da shuwagabannin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel