Rikita-Rikita: Likitoci a Arewa sun sa kafar wando daya da gwamnatin wannan jihar

Rikita-Rikita: Likitoci a Arewa sun sa kafar wando daya da gwamnatin wannan jihar

- Kungiyar likitocin kasa reshen jihar Kogi (NMA) ta bukaci membobin ta da ke jihar da su yi watsi da barazanar da gwamnatin jihar ta yi masu na korar su daga aiki idan har ba su bar yajin aiki ba.

- Kungiyar NMA ta wannan bayanin ne a cikin wani sanarwa na musamman da ya fito daga shugaban kungiyan da ke Lokoja, Dr. Tijani Godwin, inda ya ce za a cigaba da yajin aikin har idan har gwamnatin jihar bata masu bukatun su ba.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Kungiyar sannan kuma ta yi gargaji ga duk wani likita jihar da kada ya je ya sa hannu a ko wani rajista, saboda haka duk wanda ya sabawa umurnin da kungiyar ta bada zai fuskanci fushin ta domin wannan shawaran da aka yanke, an yanke shi ne da amincewar kowane memba da ke karkashin kungiyar sannan ita ce ta daure kungiyar wuri daya a yanzu.

“Mun samu labarin cewa shugaban ma’aikata (Head of Service) mai rikon kwarya, Mrs Kehinde Lawal ta bada umurni ga CMDS na HMB, KSSH da KSUTH da su bude rajista ma likitocin da suka tafi yajin aiki daga ranar Litinin 8 ga watan Mayu na shekara 2017 saboda da dokar “ba aiki ba biyan kudi”

Rikita-Rikita: Likitoci a Arewa sun sa kafar wando daya da gwamnatin wannan jihar

Rikita-Rikita: Likitoci a Arewa sun sa kafar wando daya da gwamnatin wannan jihar

“Sannan kuma an mana barazanar korar mu bisa kan aiki idan har ba mu koma aiki ba kamar yadda aka ta yadawa a kafafen yadda labarai”

“Kungiyar NMA ta umurci membobin ta da kada su razana da wannan barazanar. Ka da wani likita ya je ya sa hannu a kowane rejista da aka bude”

“Duk wani da kungiyar da ya sabawa wannan umurnin zai fuskanci fushin kungiyar saboda an riga an yanke hukuncin ba ja da baya”

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel