Kasar Faransa ta samu shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a Duniya, 39

Kasar Faransa ta samu shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a Duniya, 39

-Macron ya lashe zaben shugaban kasar Faransa

-Macron ya zama shugaban kasa mafi karancin shekaru a duniya

-Macron ya kada abokiyar takararsa da sama da kaso 65 na kuri'u

Emmanuel Macron ya lashe zaben shugaban kasar Faransa a ranar Lahadi 7 ga watan Mayu, inda ya samu nasara akan abokiyar takararsa Marine Le Pen da sama da kashi 65 na kuri’un da aka kada.

Macron ya lashe zaben ne bayan wani kutse da aka yi a shafin yanar gizon yakin neman zabensa, inda aka gano makudan sakonnin kart a kwana da aka aika masa, wanda hakan ya janyo cece kuce a kasar.

KU KARANTA: Rashin lafiya: Buhari ya bar Najeriya cikin dare; Osinbajo ya karbi ragamar mulki

Shi dai matashin shugaban kasa Macron bai taba rike wata kujerar siyasa ko na lashe zabe ba a baya, sai dai ya kasance ministan tattalin arzikin kasar Faransa na tsawon shekaru biyu.

Kasar Faransa ta samu shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a Duniya, 39

Emmanuel Macron

NAIJ.com ta gano zaben Macron da aka yi a matsayin sabon shugaban kasa ya sanya shi zama shugaban kasa mafi karancin shekaru da aka taba samu a kasar Faransa, duk da cewa matarsa nada shekaru 64, kuma ta kasance malamarsa ce a makarantar Firamari.

Kasar Faransa ta samu shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a Duniya, 39

Macron da matarsa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dan Najeriya ka kera jirgin sama

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016-
2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016- 2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel