Buhari ya sa labule da Osinbajo, Saraki da Dogara a fadar gwamnati kafin ya wuce ƙasar Ingila

Buhari ya sa labule da Osinbajo, Saraki da Dogara a fadar gwamnati kafin ya wuce ƙasar Ingila

-Shugaba Buhari ya sake komawa kasar Ingila bayan kwanaki 57 don duba lafiyarsa

-Shugaba Buhari ya gana da Osinbajo, Saraki da Dogara a fadar gwamnati

A daren jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da Kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara zuwa fadar shugaban kasa inda ya tattauna dasu tare da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Shugaban Buhari ne ya bayyana haka da kansa a shafinsa na Twitter inda ya watsa hotunan ganawar tasu, sa’annan ya kara da cewa:

KU KARANTA: Rashin lafiya: Buhari ya bar Najeriya cikin dare; Osinbajo ya karbi ragamar mulki

“Da yamman nan na samu ganawa da mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa da kaakakin majalisar wakilai akan hanyata ta fita kasar waje.

Buhari ya sa labule da Osinbajo, Saraki da Dogara a fadar gwamnati kafin ya wuce ƙasar Ingila

Buhari da Osinbajo

“Ina da tabbacin gwamnati zata cigaba da tafiya yadda ya kamata ba tare da wani tangarda ba, Allah ya albarkanci Najeriya.”

Buhari ya sa labule da Osinbajo, Saraki da Dogara a fadar gwamnati kafin ya wuce ƙasar Ingila

Buhari da Osinbajo, Saraki da Dogara

NAIJ.com ta ruwaito wata sanarwa daga fadar shugaban kasa da take bayyana cewar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai haye madafan iko a matsayin mukaddashin shugaban kasa bayan tafiyar shugaban Buhari.

Buhari ya sa labule da Osinbajo, Saraki da Dogara a fadar gwamnati kafin ya wuce ƙasar Ingila

Buhari kafin ya wuce

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Buhari zai tsaya takara a 2019? kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel