Matan Chibok: Wasu ba su da niyyar dawowa gida

Matan Chibok: Wasu ba su da niyyar dawowa gida

– Wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok ba su son su dawo gida

– ‘Yan matan sun zabi Boko Haram da su koma gidan su

– Shekaru fiye da 3 kenan da aka sace ‘Yan matan

‘Yan matan Chibok sun ce gara Shekau da iyayen su.

Don kuwa wasu ba su da niyyar komawa hannun iyayen su.

Su na ganin gara su zauna da ‘Yan Boko Haram din da su ka sace su.

Matan Chibok: Ragowar ba su da niyyar dawowa gida

'Yan Matan Chibok da aka ceto shekaran jiya

Wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok ba su son komawa gida kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ke fahimta. Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da ‘Yan Boko Haram din su ka saki ‘Yan matan na Chibok fiye da 80.

KU KARANTA: Ka ji adadin yaran da Boko Haram su ka sace

Matan Chibok: Ragowar ba su da niyyar dawowa gida

Matan Chibok sun gana da Shugaba Buhari

NAIJ.com na samun labari cewa an fara tattaunawa da ‘Yan ta’addan domin ganin an maido ragowar ‘Yan matan da su ka rage zuwa gida. Sai dai fa wasu daga cikin ‘Yan matan sun ce sun fi bukatar su zauna da ‘Yan Boko Haram din da su ka aura har su ka hayayyafa.

Bayan shekaru sama da 3 wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok din sun dawo gida yanzu bayan yarjejeniyar da aka yi tsakanin Gwamnatin tarayya da kuma shugabannin ‘Yan Boko Haram ta hannun wasu Kungiyoyi masu zaman kan su.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za a raba kasar nan ne?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel