Wasu Iyayen ‘yan matan Chibok sun kaure da murna a dandalin Unity Fountain

Wasu Iyayen ‘yan matan Chibok sun kaure da murna a dandalin Unity Fountain

- Iyayen matan Chibok sun kaure da murna yayin samu labari cewa an sake ‘yan matan 82

- Ba a baiwa ‘yan kungiyar damar su gana da ‘yan matan ba koda yake akwai wasu iyayen mata a cikin su

‘Yan kungiyar BBOG sun kaure da murna a dandalin Unity Fountain bayan labarin matan Chibok 82 da aka ceto sun shiga fadar shugaban Najeriya Aso Rock, inda suka gana da shugaba Buhari.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labara, ba a baiwa ‘yan kungiyar damar su gana da matan da aka samo sun yi gangamin murna da wasu daga cikin iyayen matan.

Ester Yakubu, na daga cikin iyayen da ‘yarta Dokas ke cikin wadanda aka sace, wadda ta ce ko cikin ‘yan matan 82 babu ‘yar ta to tana taya sauran uwaye murna. Kuma idan babu ‘yar ta yanzu gaba insha Allahu yarta zata fita.

Wasu Iyayen ‘yan matan Chibok sun kaure da murna a dandalin Unity Fountain

Shugaba Muhammadu Buhari yayin da yake ganawa da 'yan matan Chibok a fadar gwamnati

Shi kuma, Yusuf Sallau, ya nuna godiya da jin dadinsa ga shugaban ‘kasa ga wannan alkawari da ya cika, da kuma taya murna ga iyayen yaran da za su sami ‘ya ‘yansu.

KU KARANTA KUMA: Dalilan 7 da yasa Boko Haram saki ‘yan matan Chibok 82

Kasancewar kungiyar ta yi tsayin daka kan ganin cewa an ci gaba da tashi tsaye wajen nemo ‘yan matan da aka sace.

Shugaba Buhari wanda ya dauki hoto da ‘yan matan 82 cikin farin ciki ya nufi Landon don ci gaba da duba lafiyarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka tsira daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel