Mutane 2 da ake nema shugaba Buhari ya nada SGF

Mutane 2 da ake nema shugaba Buhari ya nada SGF

– Kwanakin baya Shugaba Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya

– Kusan an gama bincike game da Babachir David Lawal

– Ku na da labari cewa tuni an fara harin wannan kujera

‘Yan tsohuwar Jam’iyyar shugaba Buhari sun kawo masa sunayen wadanda ake so a matsayin SGF.

Daga ciki dai akwai tsohon Sakataren Jam’iyyar CPC a da Injiniya Buba Galadima.

Sannan kuma akwai masu marawa Cif Momoh baya.

Mutane 2 da ake nema shugaba Buhari ya nada SGF

Shugaban kasa da mukarraben sa a wai taro

NAIJ.com na da labari cewa an kawowa shugaba Buhari sunayen mutane 2 da ake so ya zaba a matsayin Sakataren gwamnatin tarayya. Wadannan mutane su ne Injiniya Buba Galadima na Jam’iyyar su ta CPC a da, da kuma Cif Tony Momoh.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya koma Asibitin Landan

Mutane 2 da ake nema shugaba Buhari ya nada SGF

Babachir Lawal ba zai dawo kujerar sa ba?

Kwamared Ikonomwan Francis da kungiyar sa su ke wannan roko wurin shugaban kasar ganin irin kokarin da su kayi a tsohuwar Jam’iyyar CPC kafin a hade. Sannan kuma cewa mutanen kirki ne marasa kwadayin abin Duniya.

Kusan ana ganin cewa Babachir Lawal ba zai dawo kujerar sa ba. Yanzu dai an fara neman wanda zai maye gurbin. Daga cikin wadanda ake tunani kuma akwai Hameed Ali da Ministoci irin su Adamu Adamu, Ogbonnoya Onu da sauran su.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda Jagoran Biyafara ya bar gidan yari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel