Rashin lafiya: Buhari ya bar Najeriya cikin dare; Osinbajo ya karbi ragamar mulki

Rashin lafiya: Buhari ya bar Najeriya cikin dare; Osinbajo ya karbi ragamar mulki

– Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma asibiti

– Shugaban kasar ya wuce Landan domin ya ga Likitocin sa

– Fadar shugaban kasar tace babu abin tada hankali

Cikin daren jiya, Lahadi, 8 ga watan Mayu ne shugaban kasa Buhari ya keta zuwa Landan.

Shugaba Buhari ya koma Landan domin ganin Likita game da jikin sa.

Farfesa Osinbajo ya karbi mulkin kasar.

Osinbajo ya karbi ragamar mulkin Najeriya

Osinbajo ya karbi mulki daga Buhari

A jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya wuce Landan kasar Ingila domin ya koma wajen Likitocin sa a asibiti. Dama tun bayan ya dawo wancan karo ya tabbatar da cewa akwai bukatar ya kara komawa nan gaba. Shugaban kasar zai dawo a lokacin da Likitoci su ka sallame sa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi amai ya lashe?

Osinbajo ya karbi ragamar mulkin Najeriya

Shugaba Buhari ya wuce Landan

Femi Adesina wanda ke magana da bakin shugaban kasar ya bayyana wannan, yace babu abin tada hankali sannan kuma mataimakin sa Farfesa Osinbajo zai ja ragamar mulkin kasar kamat yadda doka ta tanada.

Tuni shugaban kasar ya aika takarda zuwa ga majalisun kasar kana kuma ya gana da shugabannin Majalisun kasar; Yakubu Dogara da Bukola Saraki kafin ya daga zuwa Landan din. Fadar shugaban kasa ta kara jaddada cewa rashin lafiyar shugaba Buhari ba abin tada hankali bane.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wa za ka zaba tsakanin Buhari da Fayose?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel