Ra’yoyin wasu ‘yan jihar Borno game da sakin ‘yan matan Chibok 82

Ra’yoyin wasu ‘yan jihar Borno game da sakin ‘yan matan Chibok 82

- Shugabannin da mutanen jihar Borno sun tofa albarkacin bakinsu bisa nasara da aka samu kan sako wasu daga cikin ‘yan matan Chibok 82

- Gwamnan jihar Borno ya mika godiyarsa ga shugaba Mohammadu Buhari da kuma rundunar sojan kasar game da nasarar da suka samu

Biyo bayan nasarar da gwamnati Najeriya ta samu na cimma yarjejeniya da kungiyar Boko Haram, inda aka sako wasu daga cikin ‘yan matan Chibok har su 82 shugabannin da mutanen jihar Borno sun tofa albarkacin bakinsu.

NAIJ.com ta ruwaito cewa gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya yi bayani ga al’ummar jiharsa da kuma mika godiyarsa ga shugaba Mohammadu Buhari da kuma rundunar sojan kasar game da nasarar da suka samu na sake ‘yan matan Chibok.

KU KARANTA KUMA: Wasu Iyayen ‘yan matan Chibok sun kaure da murna a dandalin Unity Fountain

Da suke bayyana ra’yoyinsu wasu mazauna garin Maiduguri, kan sakin ‘yan matan Chibok da aka yi shine rashin samun cikakken bayani game da ‘yan kungiyar Boko Haram din da aka yi musayarsu da ‘yan matan 82.

Ra’yoyin wasu ‘yan jihar Borno game da sakin ‘yan matan Chibok 82

Wasu daga cikin ‘yan matan Chibok 82 a aka sake

Abin tambaya dai anan shine manene makomar mayakan Boko Haram din da aka saka? Shin zasu koma su dauki kayan yaki su ci gaba da kashe al’umma ko kum sun tuba? Yanzu dai abin da al’umma ke jira su gani shine cikakken bayanan irin yadda aka kubutar da ‘yan mata da kuma irin halin da suke ciki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga-zangar sace 'yan matan Chibok a Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dubi jerin hanyoyi da gadoji da gwamnatin APC ta ce ta kammala cikin shekaru 2

Dubi jerin hanyoyi da gadoji da gwamnatin APC ta ce ta kammala cikin shekaru 2

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel