Yan matan Chibok 82 sun gana da Buhari a fadar shugaban kasa a daren jiya (Hotuna/bidiyo)

Yan matan Chibok 82 sun gana da Buhari a fadar shugaban kasa a daren jiya (Hotuna/bidiyo)

-A daren lahadi da misalin karfe 7 ne Buhari ya gana da yan matan Chibok su 82 da aka sako

-Shugaba Buhari ya bayyana farin cikin ganinsu, tare da alkawarin cigaba da kare rayukan yan Najeriya

Yan matan chibok din nan su 82 da kungiyar Boko ta Haram ta sako a ranar Lahadi sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren jiya Lahadi 7 ga watan Mayu da misalin karfe 7:04 na dare, inji rahoton jaridar Premium Times.

Yayin dayake jawabi ga yan matan, shugaba Buhari ya tabbatar da cewar zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya kubutar da sauran yan matan Chibok din da suka rage. Buhari yace:

KU KARANTA: Dalilan 7 da yasa Boko Haram saki ‘yan matan Chibok 82

“Nayi farin ciki matuka da ganin yan matan mu sun dawo, a madadin gwamnati na, ina gode ma hukumomin tsaro, kungiyar Red Cross, hukumomin gwamnati, kungiyoyin sa kai, da duk wadanda suke da hannu cikin aikin ceton yan matan.

Yan matan Chibok 82 sun gana da Buhari a fadar shugaban kasa a daren jiya (Hotuna/bidiyo)

Buhari da yan matan Chibok

“Ina tabbatar ma yan Najeriya da iyayen sauran yan matan cewa muna yin iya kokarin mu na ganin mun kubutar da sauran da suka rage, sa’annan gwamnati zata sa idanu kan yadda za’a gudanar da aikin samar da walwala ga yan matan da aka kubutar.”

Bidiyon jawabin Buhari:

Daga karshe Buhari ya bayyana cewar gwamnatinsa zata yi dukkanin mai yiwuwa don ganin ta kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya.

Yan matan Chibok 82 sun gana da Buhari a fadar shugaban kasa a daren jiya (Hotuna/bidiyo)

Buhari na jawabi

NAIJ.com ta ruwaito muku a baya cewar gwamnati tayi musayar yan matan Chibok 82 da wasu yan ta’addan Boko Haram.

Yan matan Chibok 82 sun gana da Buhari a fadar shugaban kasa a daren jiya (Hotuna/bidiyo)

Buhari da yan matan

Ga sadda aka shigo da yan matan

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli barnar da Boko Haram tayi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel