An bayyana adadin yaran da Boko Haram su ka sace

An bayyana adadin yaran da Boko Haram su ka sace

– Majalisar UN tace ‘Yan Boko Haram sun yi mummunan ta’asa a Najeriya

– UN ta ke cewa ‘Yan ta’addan sun sace yara sama da 4000 a Yankin

– Jiya ne kuma aka gano ragowar ‘Yan matan Chibok

UN tace an sace kananan yara da dama a Arewacin Najeriya.

Boko Haram ce dai da wannan mugun barna.

Jiya aka yi musanyar wasu ‘Yan mata da Mayakan Kungiyar.

‘Yan Boko Haram sun sace yara kimanin 4000

‘Yan Boko Haram sun maido wasu matan Chibok

Yayin da ake murnar ceto ‘Yan mata 82 na Garin Chibok da aka sace kwanaki Majalisar Dinkin Duniya watau UN ta fitar da rahoto maras dadi game da ta’asar ‘yan ta’addan na Boko Haram a Yankin Arewa maso gabashin kasar.

KU KARANTA: Ra'ayin Jama'a game da ceto Matan Chibok

‘Yan Boko Haram sun sace yara kimanin 4000

Boko Haram sun yi barna a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana cewa bayan yara sama da 200 da aka sace a Makarantar nan ta Chibok shekaru 3 da su ka wuce ‘Yan Boko Haram din su sace yara kanana; maza da mata sama da 4000.

Yanzu dai ana kokarin tsare yara a Yankin kuma ma dai bugu-da-kari ana murkushe ‘Yan Boko Haram din. A Somalia kuma Jami’an tsaro sun budawa wani Minista wuta bayan da su kayi tsammanin wani Tsagera ne tuni kuwa har an birne sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An saki Nnamdi Kanu na Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel