Dalilan 7 da yasa Boko Haram saki ‘yan matan Chibok 82

Dalilan 7 da yasa Boko Haram saki ‘yan matan Chibok 82

- Dalilan 7 da yasa Boko Haram ta saki ‘yan matan makaranta Chibok 82 ga gwamnatin tarayya

- An yi wata da watanni ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da gudunmawar kungiyoyi daban-daban da kuma kasar Switzerland

A cewar rahotanni, 'yan matan makaranta Chibok 82 ne aka saki a ranar Asabar, 6 ga watan Mayu, 2017, wadanda kungiyar ta Boko Haram ta sace a watan Afrilu 2014.

Mataimakin na musammam kan harkokin yada labarai ga shugaban Najeriya, Mallam Garba Shehu ya ce a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu ne shugaba Muhammadu Buhari zai gana da 'yan matan da aka sako a fadar gwamnatin tarayya da ke birnin Abuja.

NAIJ.com ta bada jerin dalilai 7 da yasa kungiyar Boko Haram ta saki 'yan matan Chibok:

1. Sasantawa

Boko Haram ba zasu yi saki 'yan matan Chibok 82 ga gwamnatin tarayya ba tare da wata nau'i na sasantawa.

2. Musanya

'Yan Najeriya su na da ra'ayin cewa an yi musayar mayakan Boko Haram da kungiyarsu don kubutar da 'yan matan sakandaren Chibok 82.

3. Yanayin da 'yan matan suke ciki

Rahotanni na nuna cewa wasu daga cikin' yan matan nada juna biyu wasu kuma na shayar da jarirai. Yanayin da yasa ba za iya kula da su ba

4. Hadin gwiwar kungiyoyin kasar waje

Shugaba Muhammadu Buhari ya riga ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya zai gudanar da shawarwari tare da kungiyar Boko Haram ta hanyar wasu kungiyoyin kasar waje.

An yi wata da watanni ana tattaunawa da gudunmawar kungiyoyi daban-daban da kuma ita kanta kasar Switzerland.

5. Rage koken mutane da kuma yin zanga-zanga

KU KARANTA KUMA: Yadda na gudu na bar Boko Haram Inji wani Matashi

Rage koken jama'a da kuma zanga-zanga domin a saki 'yan matan Chibok ta ragu.

6. Mataki Soja a gandun dajin Sambisa

Matakin rundunar sojojin Najeriya a kan durkushe boko Haram a gandun dajin Sambisa

7. Durkushewar tattalin arzikin kasar

Koma bayan tattalin arziki a halin yanzu da ake ciki a kasar na iya sa a saki 'yan matan

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka tsira daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel