Fyade A Legas: An kama dalibai 4 da suka yi bikin fyade 'yan mata a makaranta

Fyade A Legas: An kama dalibai 4 da suka yi bikin fyade 'yan mata a makaranta

- Jami'an tsaro a jihar Legas, sun kame wasu daga cikin samarin da ake zargi laifin niyyar aikata fyade akan wasu 'yan mata na makarantarsu da ke Falomo

- Al'ada ce ayi liyafa ko biki ko sowa yayin da aka gama jarrabawar karshe ta makaranta, inda har akan sami laifukan shaye-shaye, fyade da sauran laifuka na irin samari masu wadannan shekaru

- Shaidun gani da ido sun dauki hotunan video inda aka gano 'yan matan suna kokarin tserewa mazan, amma aka tadiye su aka saka almakashi aka yayyaga musu siket, mazan kuma suka kwabe suka daura niyyar lalata da su, da ranar Allah a fili a bainar jama'a, wasu daliban kuma suna shewa suna sowa sun qara zuga su

Rahotanni daga karshe dai su nune cewa wasu masu hankali da dan tausayi sun iso wurin inda suka hana wannan aika-aika, suka kuma kwaci 'yan matan daga hannun shashashun yaran, sannan aka sanar wa da hukuma abun da ya faru. Shekarun lalatattun yaran baya wuce 15 zuwa 20, anyi nasarar chafke hudu daga cikinsu, cewar NAIJ.com

Jaridar Punch da Sahara Reporters sun ruwaito cewa, wata mata, Michelle Matthew, tana bayanin yadda abun ya auku, ta ce 'yan matan suna ta ihu, amma ba wanda ya nuna damuwa ko takaicin hakan da ke faruwa, sai ma murna da ingizawa daga 'yan kallo. cikin 'yan kallon kuwa harda security na makarantar, bassu komai sai dauka a wayoyinsu na salula.

An bada sunan yaran da ake zargi a haka, ja'iran sune, George da Abiyodun, wadanda su ake zargi da kitsa iskancin, a makarantar Ireti Grammar School. A ranar alhamis, da ta wuce, hukumar 'yan sandan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel