Babu wanda zai iya tilasta Buhari soka daga mulki

Babu wanda zai iya tilasta Buhari soka daga mulki

- Kungiyoyin tabbatar da kyakkyawar shugabanci a Najeriya ta ce babu wanda zai iya tilasta Buhari soka daga mulki

- Kungiyar ta ce kiran da ake yiwa shugaba Buhari da ya yi murabus janyewar hankali ne kawai

Kungiyoyin tabbatar da kyakkyawar shugabanci a Najeriya ta ce babu wanda zai iya tilastawa shugaban kasar Muhammadu Buhari soka daga mulki.

A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 6 ga watan Mayu, kungiyar ta ce tun da shugaban bai gayawa wani cewa ba zai iya mulkin ba, ba wanda zai iya tilasta shi ya sauka.

Kungiyar ta bayyana cewa kiran da ake wa shugaba Buhari cewa ya dauki hutu kan kiwon lafiyarsa don ganin likita a Landon, wannan wata yunkurin juyin mulkin farar hula ne.

Babu wanda zai iya tilasta Buhari soka daga mulki

Shugan kasa Muhammadu Buhari

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari , kungiyar ta ce kiran da ake yiwa shugaban kasar da ya yi murabus janyewar hankali ne kawai.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin APC na yunkurin daukar nauyin musanyar sabon dan takarar jam'iyyar don takarar 2019

Hadaddiyar kungiyar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi wa shugan kasa Muhammadu Buhari addu'ar samu lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel