Gidan da a aka gano kudade a Legas mallakar uwargidan shugaban hukumar leken asiri ne

Gidan da a aka gano kudade a Legas mallakar uwargidan shugaban hukumar leken asiri ne

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta bayyana cewa gidan da a aka gano kudade a Legas mallakar uwargidan shugaban hukumar leken asiri ne

- Hukumar ta tabbatar da haka ne a lokacin da take gabatar da shaida a wata kotu da ke Legas

- Uwargidan shugaban hukumar leken asiri ta sayi gidan a kan naira milyan 360 inda ta yi amfani da kamfanin Choba Ventures Limited

Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa gidan da aka gano makudan kudaden har dala milyan 43 a Lagos mallakar uwargidan dagakataccen shugaban hukumar leken asiri ta kasa, Misis Folashade Oke.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, hukumar EFCC ta bayyana haka ne a lokacin da hukumar ke gabatar da shaida a wata kotu da ke Legas inda hukumar ta nuna cewa Misis Folashade ta sayi gidan ne a kan naira milyan 360 inda ta yi amfani da wani kamfanin mai suna Choba Ventures Limited.

KU KARANTA KUMA: Hukumar DSS ta damke Ifeanyi Ubah akan laifin satan N11bn kudin mai

Tun da farko dai an dakatar da shugaban hukumar leken asirin, Oke Ayo bayan an gano kudaden a gidan inda ya nuna cewa kudaden mallakar hukumar leken asiri.

Gidan da a aka gano kudade a Legas mallakar uwargidan shugaban hukumar leken asiri ne

Gidan uwargidan shugaban hukumar leken asiri inda aka gano wasu kudade a Legas

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel