Idan Buhari ya gaza, Arewa za ta fito da Dan takara-Inji Okupe

Idan Buhari ya gaza, Arewa za ta fito da Dan takara-Inji Okupe

– Wani mai ba shugaba Jonathan shawara a baya yayi magana kan 2019

– Doyin Okupe yace Arewa ya dace ta tsaida dan takara idan Buhari ba zai yi takara ba

– Dr. Okupe yayi kira a guji fadin maganganu maras dadi game da lafiyar shugaba Buhari

Wani mai ba tsohon shugaban kasa Jonathan shawara a da ya bude baki game da zabe mai zuwa.

Yace idan har shugaba Buhari ba zai tsaya takara ba to ya kamata a tsaida wani Dan Arewa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ta fama da rashin lafiya.

Idan Buhari ya gaza, Arewa za ta fito da Dan takara-Inji Okupe

Arewa za ta fito da Dan takara a zabe mai zuwa-Inji Okupe

Ganin yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke fama da rashin lafiya kuma bai bayyana cewa zai tsaya takara ba. Wani mai ba tsohon shugaba Goodluck Jonathan shawara Doyin Okupe yace bai kamata kujerar ta bar Yankin Arewa ba.

KU KARANTA:

Idan Buhari ya gaza, Arewa za ta fito da Dan takara-Inji Okupe

Ko Buhari ba zai iya ba, Arewa za ta cigaba da mulki

Dr. Okupe yace idan har Shugaba Buhari ya gagara tsayawa takarar sai a dauko wani daga Yankin Arewacin kasar yayi takara. Okupe yace tun dawowa Damukaradiyya Arewa tay shekaru 4 tana mulki yayin da kudancin kasar sun yi 14.

Doyin Okupe yayi kira da Jama’a su fadi alheri game rashin lafiyar shugaban kasar wanda babu wanda ya fi karfin hakan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wa za a zaba a zabe mai zuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel