Mun yi musayar mayakan Boko Haram da kungiyarsu don kubutar da 'yan matan Chibok 82 – Inji Gwamnati

Mun yi musayar mayakan Boko Haram da kungiyarsu don kubutar da 'yan matan Chibok 82 – Inji Gwamnati

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta yi musayar mayakan Boko Haram da kungiyarsu don kubutar da 'yan matan Chibok

- Mallam Garba Shehu ya ce yau Lahadi, 7 ga watan Mayu ne shugaba Muhammadu Buhari zai karbi 'yan matan Chibok 82 da aka sako.

- Shehu ya ce an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da su 'yan kungiyar Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi musayar mayakan Boko Haram da kungiyarsu don kubutar da 'yan matan sakandaren Chibok 82, a ranar Asabar 6 ga watan Mayu.

A baya ma, kungiyar 'yan tada-kayar-baya Boko Haram ta saki 'yan matan Chibok guda 21.

NAIJ.com ta ruwaito cewa sama da shekara 3 kenan da sace 'yan makarantar sakandaren kusan 300 a garin Chibok na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Mun yi musayar mayakan Boko Haram da kungiyarsu don kubutar da 'yan matan Chibok 82 – Inji Gwamnati

Shugaba Buhari da wasu 'yan matan Chibok

Mataimakin na musammam kan harkokin yada labarai ga shugaban Najeriya, Mallam Garba Shehu ya ce a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu ne shugaba Muhammadu Buhari zai karbi 'yan matan da aka sako a fadar gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram ta saki yan matan Chibok 82

An yi wata da watanni ana tattaunawa da gudunmawar kungiyoyi daban-daban da kuma ita kanta kasar Switzerland.

Wannan tattaunawa da aka yi, sai aka cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya da su 'yan kungiyar, wanda gwamnati ta karbi 'yan matan.

Shehu ya ce su kuma aka basu wasu daga cikin magoya bayan kungiyarsu da ke hannun gwamnatin tarayya a yanzu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon zanga-zangar tunawa da 'yan matan Chibok bayan kwanaki 500 a hannun boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel