Yadda aka dawo da ‘Yan matan Chibok gida

Yadda aka dawo da ‘Yan matan Chibok gida

– Sahara Reporters ce ta fara zakulo maganar sakin ‘Yan matan

– Yanzu haka Boko Haram sun saki ‘Yan matan na Chibok fiye da 80

– An dai dade ana ta kokarin kulla yarjejeniyar hakan

Yanzu haka kuna da masaniyar cewa ‘Yan matan Chibok 82 sun bar hannun Boko Haram.

Shekaru fiye da 3 kenan da aka yi gaba da ‘Yan makarantar.

Sahara Reporters ta bayyana yadda aka yi wajen sakin ‘Yan matan.

Yadda aka dawo da ‘Yan matan Chibok gida

Boko Haram sun saki ‘Yan matan Chibok

Bayan shekaru sama da 3 wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok za su dawo gidajen su. An dai ta kokarin yarjejeniya tsakanin Gwamnatin tarayya da kuma shugabannin ‘Yan Boko Haram ta hannun wasu ‘yan kungiyar da ke tsare.

KU KARANTA: An saki 'Yan matan Chibok

Yadda aka dawo da ‘Yan matan Chibok gida

‘Yan matan Chibok da aka sace

An dai kuma yi amfani da Hukumar DSS da Kungiyar Red Cross ta Duniya wajen karbar ‘Yan matan na Chibok da ke hannun Boko Haram a wani kauye da ake kira Banki. Bayan nan ne Sojojn Najeriya su ka samu ceto matan har su 82.

Kwanaki yayin da Yemi Osinbajo ke jan ragamar kasar ‘Yan Kungiyar nan masu fafutukar ganin ‘Yan matan nan na Chibok sun dawo gida watau BBOG sun tasa Farfesa Osinbajo a gaba game da yaran.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Waye na zaba: Fayose da Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel