‘Yan Najeriya ku ceci ran wannan mahaddacin Kur'ani (Hotuna)

‘Yan Najeriya ku ceci ran wannan mahaddacin Kur'ani (Hotuna)

- Malam Nayif Isma'il yana fama da ciwon koda wanda a yanzu ana yi mishi wankin koda sau biyu a sati

- Ana bukatar taimakon gaggawa daga al’umma don sai an fita da shi waje a yi mishi dashen koda

- Likitoci sun ce akalla aikin zai ci kimanin naira miliyan 10

Jama'a gini akan hadisin da Annabi alaihissalam yace : musulmai kamar gini guda suke, sashinsu yana karfafar sashi, idan gaba daya ta kamu da ciwo duka gangar jiki sai fara daukar zazzabi da masasshara.

Dogaro da wannan hadisi muke sanar da al'umma, akwai yaro qaninmu dalibin ilmi hafizin Alqur'ani da yake fama da ciwon koda, wanda a yanzu haka yana asibitin Nassarawa ana yi mishi wankin koda (dialysis ) sau biyu a sati, ga ciwon ya yi tsananin da sai an fita da shi waje an yi mishi dashen koda, wanda ake neman zunzurutun kudi dalar Amurka 13,500 wanda a canjin kudin Najeriya ya doshi miliyan 10, don haka a na neman taimakon 'yan uwa gwargwadon ikon kowa.

KU KARANTA KUMA: An caccaki Anthony Joshua saboda yayi Sallah a Masallaci

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sunan yaron: Nayif Isma'il, dan Fagge ne layin malam Umar sani Fagge, malami ne mai koyar da Alqur'ani a makarantar Ansarussunnah Fagge da ke jihar Kano.

‘Yan Najeriya ku ceci ran wannan mahaddacin Kur'ani

Nayif Isma'il, dan Fagge a layin malam Umar sani Fagge, na neman taimakon gaggawa daga al'umma musulmai

Malam Nayif Isma'il na neman taimakon gaggawa ga al'umma akan a taimaka masa.

Ga mai bukatar taimakawa da abinda ya samu ga account din yayanshi Shakeeki kamar haka:

Account name: Assad Isma'il Zakariyya,

Bank: first bank,

Acct. No: 3019347746

Acct. type: saving

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel