Fasinjoji 36 sun hallaka, jariri 1 ya tsira yayinda motoci biyu sukayi kicibis a titin Lagos-Ibadan

Ana tsoron akalla mutane 36 sun rasa rayukansu a yau Asabar 6 ga watan Mayu yayinda wasu motocin haya 2 sukaci karo da juna kuma suka kama da wuta a Quarry site Km 96, Lagos-Ibadan Expressway.

Wani idon shaida yace, motocin masu iya daukan fasinja 18 sunyi kicibis ne kuma suka kama da wuta a take.

Fasinjoji 36 sun hallaka, jariri 1 ya tsira yayinda motoci biyu sukayi kicibis a titin Lagos-Ibadan

Fasinjoji 36 sun hallaka, jariri 1 ya tsira yayinda motoci biyu sukayi kicibis a titin Lagos-Ibadan

“Dukkan fasinjojin da ke cikin moton sun kone kurmus. Jariri daya ne kawai ya tsira saboda mahaifin ya jefo yaron ta tagar mota.

KU KARANTA: NNPC tace ba zata dauki ma'aikata ba

Kwamandan hukumar tsaron hanyar mota, shiyar jihar Oyo, Mr Yusuf Salami, ya tabbatar da wannan labari.

Amma Salami yace har yanzu ba’a fada masa yawan mutanen da suka hallaka ba

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

NAIJ.com
Mailfire view pixel