Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin hukuncin daurin rai da rai ga wanda ya fyade jaririya

Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin hukuncin daurin rai da rai ga wanda ya fyade jaririya

Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin cewa duk wanda ke da hannu cikin zancen fyaden yar wata 6, ya zauna a kurkuku tsawon rayuwarsa.

Gwamnatin tace ranta yayi matukar baci da labarin cewa wani makusancin dangin ne yayi ma jaririya fyade.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a wata jawabin da kwamishanan yad labaran jihar, Malam Mohammed Garba, ya saki yau Asabar.

Tace gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umurci ma’aikatar shari’ar jihar ta tabbatar da cewa an hukunta wada ya aikata wannan laifi.

Fyaden jaririyar wata 6 : Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin hukuncin daurin rai da rai

Fyaden jaririyar wata 6 : Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin hukuncin daurin rai da rai

Gwamnatin ta zayyana cewa wannan ya nuna rashin imanin wanda ya aikata wannan laifi kuma ya cancanci ukubu mafi tsanani.

KU KARANTA: Rashin hankali ne cewa Buhari yayi murabus - Okupe

Jawabin tace gwamnati zata biya kudin asibitin kuma ta baiwa iyayen yarinyar shawara kan lura da wanda zasu zauna da shi a asibitin.

Tayi kira ga malaman addini suyi amfani da wajajen bautansu wajan bayyana illan irin wannan laifi ga al’umma.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel