Bamu daukan aiki yanzu - NNPC

Bamu daukan aiki yanzu - NNPC

Babban kamfanin man feturin Najeriya wato Nigeria National Petroleum Corporation (NNPC), ta jaddada cewa mutane suyi watsi da dukkan masu cewa ana daukan aiki a kamfanin.

Shugaban sashen yada labarai, Mr Ndu Ughamadu, ya bayyana wannan ne a wata jawabin da ya saki ranan Juma’a a Abuja.

Game da cewarsa, wannan shine karo na uku da ake yada jita-jitan cewa kamfanin zata dauki ma’aikata.

Bamu daukan aiki yanzu - NNPC

Bamu daukan aiki yanzu - NNPC

“Muna sake sanar da cewa, NNPC bata daukan ma’aikata a yanzu.”

” Saboda haka, muna baiwa jama’a shawaran cewa suyi watsi da dukkan wani sanarwa na kafafen yada labarai cewa zamu dauka. Wannan aikin yan damfara ne domin kokarin cutan yan Najeriya.”

KU KARANTA: Rashin hankali ne cewa Buhari yayi murabus

”Duk wanda ya bari wasu suka gayyaceshi zuwa wani mu’ayanan aiki wannan ruwanshi ne,”.

Yace duk wanda ya samu irin wannan sanarwa ta aiki ba a cikin jaridun Najeriya bay a kai kara ofishin jami’an tsaro.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel