Hukumar kula da kwallon kafa ta FIFA ta amince Messi ya ci gaba da wasa

Hukumar kula da kwallon kafa ta FIFA ta amince Messi ya ci gaba da wasa

- Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta dage dokar haramcin wasa hudu da aka sanya wa Lionel Messi, wanda hakan ke nufin a yanzu zai iya wakiltar kasarsa a wasan neman gurbin gasar kofin duniya.

- An kori dan wasan gaba na Barcelonan saboda ya furta "kalaman zagi" ga mataimakin alkalin wasa, lokacin da kasa Argentina ta ci kasar Chile 1-0 a watan Maris.

Dan wasan mai shekara 29, bai buga wasan da kasar ta sha kashi a hannun Bolivia da ci 2-0 ba.

NAIJ.com ta samu cewa kwamitin daukaka kara na Fifa ya ce, abun da dan wasan ya yi, "Sam bai dace ba," to amma hujjar ba ta isa a yi masa wannan hukunci ba.

Yanzu dai dan wasan zai buga wasannin da kasar za ta fafata da Uruguay, da Venezuela da kuma Peru, yayin da kasar ke fatan samun gurbi a gasar kofin duniya da za a yi a kasar Rasha a shekara mai zuwa.

Hukumar kula da kwallon kafa ta FIFA ta amince Messi ya ci gaba da wasa

Hukumar kula da kwallon kafa ta FIFA ta amince Messi ya ci gaba da wasa

KU KARANTA: Mai maganin gargajiya ya bukaci a bashi dama ya ba Buhari Magani

Haka kuma an dage tarar fam 7,800 da aka sanya wa dan wasan.

An dai nuno Messi a kamara yana nuna fushinsa ga mataimakin alkalin wasa, wanda ya nuna cewa Messi ya yi laifi lokacin wasan da kasar ta yi nasara a kan Chile.

Haka kuma a wata sanarwa da kwamitin ya fitar ya ce, nuna da'a ga alkalan wasa na da matukar muhimmanci, kuma saba wa wannan doka babban laifi ne, kuma abu ne da ba za a lamunta ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel