Rundunar yan sandan Najeriya ta kama wani Fasto da kan mutum

Rundunar yan sandan Najeriya ta kama wani Fasto da kan mutum

- Rundunar yan sandan Najeriya shiyyar jihar oyo ta bayyana a ranar juma'ar da ta gabata cewa sun samu nasarar damke wani babban Fasto da kan mutum.

- Sauran abubuwan da suka kama tare da Fasto din hadda kan wata dabbar namun daji da kuma bindiga.

Haka ma dai rundunar yan sandan jihar ta kama wasu mutane 18 da suke zargi da laifin sata da fashi da makami sannan kuma da shiga kungiyar asiri.

NAIJ.com ta samu cewa Kwamishinan yan sandan jihar ya bayyana cewa shi dai Faston shine ya assasa cocin Cherubim da kuma cocin Seraphim, Idapomimo Zion, Alagbado, duka dake a garin Lagas.

Rundunar yan sandan Najeriya ta kama wani Fasto da kan mutum

Rundunar yan sandan Najeriya ta kama wani Fasto da kan mutum

A wani labarin Rundunar yan sanda a jihar Taraba ta bayyana cewa ta samu nasarar kama wani dan shekara 60 mai suna Abubakar Abdulkadir da sassan jikin dan adam.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Mr David Misal shine ya bayyana hakan a jiya juma'a a ofishin yan sandan dake a garin jalingo.

Yan sandan sunce ana ma tunanin cewa soyayyen naman na mutun din da aka gan sa da shi na wani dan uwan sa ne mai suna Ali Gimba wanda aka bayyana bacewar sa tun 27 ga watan Afrilu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel