Hadarin mota ya rutsa da wata mata kwanaki 4 kafin bikinta

Hadarin mota ya rutsa da wata mata kwanaki 4 kafin bikinta

- Wata mace yar shekara 20, da aka bayyana sunanta a matsayin Rukayya,wacce aka shirya daura aurenta a yau Asabar ta rasa ranta sakamakon markadeta da wata mota tayi

- Anyi hadarin ne a garin Abaji dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Wata mace yar shekara 20, da aka bayyana sunanta a matsayin Rukayya,wacce aka shirya daura aurenta a yau Asabar ta rasa ranta sakamakon markadeta da wata mota tayi a garin Abaji dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Wani shaidar gani da ido mai suna Aliyu, yace matar tana kan babur din achaba, sai tayar babur din ta fashe inda suka fadi a tsakiyar titi, direban babur din ya samu kaucewa daga titin yayin da ita kuma wata mota kirar J5 ta markadeta har lahira.

Hadarin mota ya rutsa da wata mata kwanaki 4 kafin bikinta

Hadarin mota ya rutsa da wata mata kwanaki 4 kafin bikinta

KU KARANTA: Jigo a PDP ya bukaci Buhari yayi murabus

NAIJ.com ta samu labarin yace direban motar ya tsere, ya bar tarkacen naman jikin matar warwatse a kan titin. Jami’an hukumar kiyaye hadura ta kasa ne suka dauki gawar matar zuwa asibitin Abaji kana daga bisani suka mika ta ga yan uwanta domin ayi mata jana’iza.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa matar tafito ne daga garin Shafa -Abakpa dake karamar hukumar Toto ta jihar Nassarawa, kuma tazo Abaji ne domin sayan kayayyakin bikinta da za’ayi a ranar Asabar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel