Kakakin majalisan wakilai ya biya kudin asibitin maras lafiya kimanin N4 million

Kakakin majalisan wakilai ya biya kudin asibitin maras lafiya kimanin N4 million

Kakakin majalisan wakilan Najeriya, Yakubu Dogara, ya tafi mazabarsa da ke Bauchi domin kaddamar da wasu ayyukan da yayi kuma ya kai ziyara asibitin jihar.

Jaridar NAIJ.com ta samu wannan labara ta shafin ra’ayin kakakin ta Fezbuk inda ya bayyana hakan, yace:

“A yanzu haka ina jihar Bauchi domin kaddamar da wasu ayyukan mazabata – wanda kuma zai amfani jihar gaba daya.

Inda na fara ziyara shine asibitin jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) inda muka bayar da taimako ga maras lafiyan da ke wurin ta hanyar biyan kudin asibitinsu.

Kakakin majalisan wakilai ya biya kudin asibitin maras lafiya kimanin N4 million

Kakakin majalisan wakilai ya biya kudin asibitin maras lafiya kimanin N4 million

Mun bayar da wannan taimako ne saboda matsin tattalin arzikin da yawancin Najeriya ke fuskanta. Kana kuma harkan kiwon lafiya abu ne mai muhimmanci kuma nayi farin cikin ganin yadda abubuwa ke gudana a jami’ ar.

KU KARANTA: Buhari yayi murabus kawai - Fani-Kayode

Taimakon da muka bada, kimanin N4 million, hadin kan dukkan yan majalisan da ke wakiltan jihar Bauchi ne – Sanatoci da yan majalisan wakilai da kuma wasu yan majalisan kwarai wadanda suka taimakawa maras lafiya.

Kana na gana da shugabancin asibitin kuma munyi bayanin yadda za’a samo tallafi ga asibitin ATBU da FMC, Bauchi, saboda sune asibitocin gwamnatin tarayya 2 a jihar.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel