Gunaguni a kan kiwon lafiya Buhari

Gunaguni a kan kiwon lafiya Buhari

- Kungiyar goyon bayan shugaba Buhari ta yi tir da gunaguni a kan kiwon lafiyar shugaba Buhari

- Kungiyar ta ce gunaguni daga ‘yan baranda siyasa ne kawai don kawo tikas ga kokarin shugaba Buhari da yaki da cin hanci da rashawa

Wata kungiyar goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buahri, Buhari Media Support Group (BMSG) ta zargi wasu kungiyoyi da kuma daidaikun mutane a kasar da yin siyasa da kiwon lafiya shugaba Buhari.

NAIJ.com ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa a ranar Alhamis, 4 ga watn Mayu, cewa masu gunaguni a kan kiwon lafiyar shugaban kasar da nufin su janye hankalin mutane daga yaki da cin hanci da rashawa.

KU KARANTA KUMA: Jerin kayayyaki 40 da gwamnati ta hana shigo dasu Najeriya

Kungiyar ta ce ‘yan Najeriya yanzu na yaba wa shugabancin shugaba Buhari da kuma ayyukokin da gwamnatin tarayya ke aiwatar a duk fadin kasar.

Gunaguni a kan kiwon lafiya Buhari

Shugaban Buhari kan hanyarsa zuwa masalacin juma'a

Kungiyar ta lura da cewa gunaguni a kan kiwon lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari zance ne kawai daga ‘yan baranda siyasa don dakile kokarin shugaba Buhari daga yaki cin hanci da rashawa a kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon murnar dawowar shughaban kasa Muhammadu Buhari daga Landon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel