Jerin kayayyaki 40 da gwamnati ta hana shigo dasu Najeriya

Jerin kayayyaki 40 da gwamnati ta hana shigo dasu Najeriya

-Gwamnatin Najeriya ta haramta shigo da wasu kayayyaki wadanda za'a iya hada su a gida

-Babban bankin Najeriya ta haramta bayar da canjin dala ga yan kasuwannin dake shigo da haramtattun kayan

Babban bankin Najeriya ya nanata dokar haramta shigo da wasu kayayyaki guda 40 gida Najeriya, tare da hana bayar da canjin dala ga duk wanda ke harkar shigo dasu.

Bankin ta sanar da haka ne a ranar Alhamis 4 ga watan Mayu ta hannun daraktan watsa labarum ta Isaac Okorafor a garin Abuja.

KU KARANTA: Dillalan motoci a jihar Kaduna sun banka ma motar Hukumar Kwastam wuta

Isaac yace “Babban bankin Najeriya bata janye dokar hana canjin dala ga duk yan kasuwan dake shigo da haramtattun kayayyaki ba, ba kamar yadda ake yadawa a kafafen sadarwa wai mun janye dokar ba.”

Jerin kayayyaki 40 da gwamnati ta hana shigo dasu Najeriya

Gwamnan babban banki

NAIJ.com ta kawo muku jerin kayayyakin da gwamnatin tarayya ta hana shigo dasu Najeriya da suka hada da:

Shinkafa

Siminti

Man bredi

Man ja

Ganye

Kaji da kwai

Turaren India

Kifin gwangwani

Karafa

Hadaddun karafa

Kwanon rufi

Baro

Kwangiri

Sundukai na karfe

Kayayyakin kicin

Durom

Bututun karfe

Rodi

Murdaddun rodi

Wayoyin karfe

Kusoshi

Wayar kariya daga barayi

Hadaddun katako

Fulai wood

Kofofin katako

Tsinken sakace

Gilasai

Kayan amfani a kicin

Kwanuka da kofuna

Tayil

Atamfa da yadi

Shadda

Gwanjo

Ledoji

Sabulai

Kayan shafa

Tumatirin leda

Kudaden kasashen waje

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kayayyaki yayi tashin gwauron zabi a kasuwanni

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel