An yanke hukunci zaman kurkukun shekara 7 ga mutumin yayiwa yar shekara 12 fyade

An yanke hukunci zaman kurkukun shekara 7 ga mutumin yayiwa yar shekara 12 fyade

Jastis Maruf Adegbola na babban kotun Ibadan da ke jihar Oyo, yau Juma’a ya aika wani Gafar Asimiyu zama gidan yarin shekaru 7 kan fyaden yar shekara 12.

Adegbola yace hujjan da aka kawo akansa ya nuna cewa ya aikata laifin fyade.

“Rahoton asibtin Adeoyo ya nuna cewa an keta farjin yarinyar da akayiwa fyade.”

Kana kuma yace a wata jawabi cewa abun laifin bai musanta hakan ba, kuma wannan ya taimaka wajen karfafa hujja akanshi.

An yanke hukunci zaman kurkukun shekara 7 ga mutumin yayiwa yar shekara 12 fyade

An yanke hukunci zaman kurkukun shekara 7 ga mutumin yayiwa yar shekara 12 fyade

“Jawabin da abun zargin yayi ga dan sanda mai bincike ya nuna cewa mai laifin yayi jima’I da yarinyan ba tare izininta da sonta ba."

Adegbola yace duk da cewan sashe 259 na dokar jihar Oyo ya yanke hukuncin zaman gidan yarin rai da rai, ya aikashi shekaru 7 kacal.

KU KARANTA: An yankewa barayin shanaye 3 hukuncin kisa

Lauyan yarinyan Mr Olayiwola Oloso, ya fadawa kotu cewa Asimiyu ya aikata wannan laifine ranan 18 ga watan Fabrairun 2013 a Ibadan.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel