An yi arangama tsakanin magoya bayan kwankwaso da na Atiku Abubakar a garin Jada

An yi arangama tsakanin magoya bayan kwankwaso da na Atiku Abubakar a garin Jada

- Akalla mutane 10 suka ji rauni a wata arangama tsakanin magoya bayan kwankwaso da na Atiku Abubakar a garin Jada dake jihar Adamawa a wajen taron bikin nadin sarauta

- An kai hari a kan mambobi Kwankwasiyya Movement na garin Jada wadanda ke goyon bayan sanata Rabiu Kwankwaso

Wasu mutane da ake zato magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar sun yi arangama da masu goyi bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, a kan zaben shugaban kasar na 2019.

Bincike ya nuna cewa lamarin wanda ya auku a ranar Alhamis, 4 ga watan Mayu ya samo asali ne a yayin da gwamnan jihar Adamawa Bindow da Atiku suka ziyarci garin Jada dake jihar Adamawa domin halartar bikin nadin sarauta.

Mazauna garin sun shaida wa NAIJ.com cewa magoya bayan Malam Abubakar da gwamnan Adamawa, Mohammed Jibrilla, sun kai hari ga wasu matasa domin saka jar hula domin nuna goyon bayan su ga tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Kwankwaso.

An yi arangama tsakanin magoya bayan kwankwaso da na Atiku Abubakar a garin Jada

Daya daga cikin magoya bayan sanata Rabiu Kwankwaso a asibiti

KU KARANTA KUMA: Kaji abunda EFCC ta samu da ta kai farmaki gidan Kwankwaso?

Mambobi Kwankwasiyya Movement a garin aka kai wa hari wadanda ke goyon bayan sanata Rabiu Kwankwaso, wanda ake sa ran zai yi takarar shugaban kasar a 2019.

Akalla mutane 10 suka ji rauni. Wani mazaunan garin malam Bamanga Mohammed ya ce, abin bakin ciki ne cewa wasu sun shigo da 'yan baranda daga wani jiha don tada zauna tsaye saboda banbancin siyasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tsakanin gwamna Fayose da shugaba Buhari, wa za ku zaba a 2019?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel