Rikici: Kungiyar CAN ta bukaci gwamnatin Jihar Kaduna da ta sake bude jami'o'i 3 na kudancin Jihar

Rikici: Kungiyar CAN ta bukaci gwamnatin Jihar Kaduna da ta sake bude jami'o'i 3 na kudancin Jihar

- Shugaban kungiyar CAN, Ayokunle yayi kiran ne ga gwamnatin Kaduna a yayin wata ziyara da ya kai domin raba kayan agajina kimanin kudi naira miliyan takwas ga wadanda rikicin ya jikata

- CAN tayi kira da babbar murya akan gwamnatin tarayya tayi kokarin daukan matakin magance sake aukuwar rikici a yankin da sauran yankunan kasa baki daya

Shugaban CAN na Najeriya Rabaren Samson Ayokunle, a Kafanchan (Jihar Kaduna) a 4 ga watan Maris shekarar 2017 ya nema daga gwamnatin Jihar kaduna da ta sake bude babbar makarantar da aka rufe sakamakon rikicin yankin kudancin Jihar.

Ayokunle yayi kiran ne a ranar Alhamis a kafancan a yayin wata ziyara da ya kai domin raba kayan agajina kimanin kudi naira miliyan takwas ga wadanda rikicin ya raunata ko ya jikata.

A daga majiyar da NAIJ.com ta samo makarantun uku da aka rufe shekarar da ta gabata na yankin sune – Kafanchan kampus na na jami'ar Kaduna, kwalejin karantarwa na Gidan-Way, da kwalejin Nursing na Kafanchan.

An rufe makarantun ne a lokacinda suke daf da su kare karatun shekarar 2016/2017.a jawaban Ayokunle,ya nuna matukar mamaki gameda kin bude makarantun har kawowar yanzu kuma ya bada shawarar gwamnati ta waiwayi abin don kada karatun yaran ya tozarta.

KU KARANTA: Tsammani abin da wannan kungiyar addini sun shirya bisa kiwon lafiya Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban na CAN yayi kira da babbar murya akan gwamnati tayi kokarin daukan mataki magance sake aukuwar rikici a yankin da sauran yankunan kasa baki daya don tabbatar da wanzuwar zama lafiya.

Ya ce: ''Ina rokon gwamnatin jihar kaduna da ta sake bude wadannan makarantu, sannan a tabbatar da tsaro ga daliban"zama lafiyan najeriya ya kunshi zama lafiyan dukkanin yankokin kasar.''

Yace ziyarar ta kunshi nuna kauna da kokawa yan'uwa da rikicin ya cika dasu ta hanyar bada tallafin kayan dolen rayuwa a garesuAyokunle ya kara nema daga gwamnatin jihar da ta taimaka gurin sake gina cocinan da aka bata sakamakon rikicin tareda kama wadanda suka yi wannan aika aikan.

A karshe ya yabawa gwarzantaka da jami'an tsaro keyi na yau da kullum,kuma ya kara da karfafarsu a cigaba da aikinsu.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel