Yeh! Babbar adadin kudi da gwamnatin Jonathan ta kashe akan haƙa kogin Neja zai buga ka

Yeh! Babbar adadin kudi da gwamnatin Jonathan ta kashe akan haƙa kogin Neja zai buga ka

- Goodluck Jonathan ya biya wata kwangila biliyan N34 don haƙa kogin Neja

- Gwamnati Muhammadu Buhari ya bayar miliyan N100 kawai a kan aikin

- Mutane suna mamaki yadda za mu iya haƙa kogin Neja tare da miliyan N100

- Shugaba Buhari ya amince da miliyan $186 domin yaki da 'yan fashin teku

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ce tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya biya wata kwangila biliyan N34 don haƙa kogin Neja, kuma kamfanin ya gaza yin aikin. A cewar sa, gwamnati Muhammadu Buhari ya bayar miliyan N100 kawai a kan aikin.

NAIJ.com ya samu labari cewa, Amaechi ya sanya wannan da'awar a lõkacin da ya yi magana a wani taro kan saurin gyaran tashar jiragen ruwa wanda gidan jarida ‘The Nation’ ya shirya tare da ma'aikatar sufuri da kuma kamfanin Epsilon a ranar Alhamis, 4 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Bararayin Shanaye 3 zasu fuskanci Hukuncin Rataya a kotu

Ya ce: "Lokacin da gwamnatin da ta gabata, ta farko amince a haƙa kogin Neja, ta amince ne da biliyan N47 sai suka biya biliyan N34 ma kwangila. Aka kira masu rawa sai ana ta yin biki. Muna haƙa Kogin Neja yanzu, ba da biliyoyin Nera ba, muna haƙa Kogin Neja ne tare da miliyan N100 kawai.

"Lokacin da muka masa alamar fara aikin wajen kwanan nan, ka gani muna rawa? Mun yi biki? Na yi tafiya wajen ne kawai zuwa ga gwamnan na gaya masa cewa aikin zai fara a yau kuma za a gama a wata guda.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ce tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya biya wata kwangila biliyan N34 ga haƙan Kogin Neja, kuma kamfanin ya gaza yin aikin

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ce tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya biya wata kwangila biliyan N34 ga haƙan Kogin Neja, kuma kamfanin ya gaza yin aikin

"Gwamnan ya ce zai bi ni, kuma na ce ba damuwa'. Saboda haka, na ce Gwamnan tayar da aikin tun da a jiharsa ne."

KU KARANTA: Za’a ci tarar duk wanda ya ci mutuncin tutar Najeriya maƙudan kuɗi, Karanta

Ya ci gaba: "Mutane suna mamaki yadda za mu iya haƙa Kogin Neja tare da miliyan N100 da gwamnatin da suka gabata sun bayar da wannan kwangila a biliyan N47? Amma za mu haƙa kogin Neja, ta amfani abin haƙa rafi wanda ya kasance mallakar ‘National Inland Waterways Authority’ (NIWA).

"NIWA na da abin haƙa rafi, gwamnatin da sun fĩfĩta ba masu kwangila kudi su haƙa kogin tare da masu abin haƙa kogi na zaman kansu yayin da na NIWA na kwance a wani wuri a jihar Ribas.

KU KARANTA: Binciken yansanda a gidan Kwankwaso: “Gwamnati tayi taka tsan-tsan” - Kwankwaso

"MD na NIWA ya ce mini kamfanin na da abin haƙa kogi, amma an yi hayar ma wani a jihar Ribas. Saboda haka, muna da abin haƙa kogi , amma gwamnati da sun hayar da su wa wasu mutane a Ribas yayin da suna biyan mai kwangila biliyoyin Nera don amfani da wani daban.

"Na shaida wa shugaban NIWA cewa zan nemi kudi na zuba man a abin haƙa, kuma aiki ya fara. Wannan shi ne dalilin da ya sa muna haƙa kogin Neja tare da miliyan N100 kawai."

Amaechi ya ce Shugaba Buhari ya amince da miliyan $186 domin yaki da 'yan fashin teku da kuma sauran masu aikata laifi a kan ruwa.

Sashe na daga cikin kudi, ministan ya ce, za a kashe a kan jirage 3 masu saukar ungulu da kuma jirgin sama 3, da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A wannan NAIJ.com bidiyo, Amaechi na cewa suna kan titi suna aiki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel